Amfanin Tunfafiya Ga Lafiyar Jikin Dan Adam.

0 4,861

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Muhimman Wasu Bangarori Na Jikin Tunfafiya

Tunfafiya abace wacce kusan kowa yasanta, sannan yawancin mutane akan gaya musu cewa baason zuwa wurin kasancewar a cewarsu tanada aljanu, ammabkuma wasu basu sani ba akan cewa tanada matukar amfani a jikinsu.

Tunfafiya kan fito a wurare daban daban a wuraren mu amma mafiya yawanci anfi samunta a daji kokuma wani kango daya dade mutane basa zuwa. Haka zalika mutanane da can sunfi amfani da Tunfafiya wajen maganin cututtuka a jikiinsu saboda finmu sanin mahimmancinta.

Wannan rubutu da mukai munkawo magungunan da wannan bishiya takeyi.

Domin Magance Ciwon Hakori:


Sai a nemi ganyen tunfafiya mai kyau da fatar lemon tsami sai a tafasashi sosai ya tafasu wurin tafashen a zuba dan gishiri sai a dinga kuskure baki dashi.

Yana maganin ciwon hakori da wasu cututtuka da dama daya shafi baki.

Rashin Ji Sanadin Wata Rashin Lafiya:


Zaa samu yallon na ganyen tunfafiya sai a markadashi sosai, a tafasashi sosai a barshi yayi sanyi sai a tace shi sai dinga wanke kunne dashu tsawon Sati biyu ko uku zaa samu lafiya da yardar Allah.

Domin Magance Basir Mai Tsiro:


Zaku samu ganyen tunfafiya kushafa man shafawa a jiki saiku karashi a wuta yadanyi zafi saiku dinga dannawa a dubura inda ciwon ya fito.

Domin Magance Ciwon Makero:

Ana diga ruwan tunfafiya wanda idan anciro ganyenta za’aga yana fitar da wani farin ruwa. Za’a samu mai ciwon makeron sai a kankare yadan fara jini sai a diga wannan farin ruwan a kai, za’a dinga yin haka duk bayan kwana biyu ko uku.

Mai Tarin Fuka Dana Asma:

Zaa samu ganyen tunfafiya sai shanyashi ya bushe, sai a dinga yin turare dashi.

Domin Gyaran Fata.


Zaku samu ruwan tunfafiya farin nan saiku hadashi da man Kadai saika gaurayasu baki daya, kadinga shafasu duk lokacin dakayi wanka. Maana yazama kamar man shafawarku.

Yana maganin cututtuka na fata kamar: kaikayin jiki, kuraje Jiki Zaa shafa a inda kurajen jiki.

Domin Magance Wani Bangare Na Jiki Daya Mutu Ko Yake Gaf Da Mutuwa.

Zaku samu bawo tunfafiya kushanya ya bushe sosai saiku samo kitsen damo a hadashi kamar man shafawa a dinga shafawa a wurin matsalar.

Domin Magance Tsutsar Ciki.


Kunemi furen tunfafiya saiku nikashi ya nuku sai a tafasashi yatafasu sai tace shi kusamu zuma mai kyua a zuba a ciki a dinga sha.

Domin Maganin Mayu.


Sai asmo furen Tunfafiya a bude cikinta akwai wani kwallo sai cinyeshi duk.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »