Kyawawan Sunonin Annabi SAW 11 Ranar Idi

0 470

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sallar Idi sallah ce dake zuwa duk shekara gata kuma da tarin lada masu dubbin yawa musan man ace anyita ko gudanar da ita yadda ta hanyar bin sunonin Annabin tsira Sallallahu Alaihi Wassalam ya tsarata.

Wannan dalili yasa muka zaliko wasu sunoni Annabi S A W guda shadaya don tunatar da bayin Allah, kuma zaka iya taba hoton don kasaukar a wayarka ka dora a WhatsApp status naka don tunawa wasu kuma kaima kasamu ladan tunatarwa, Sunonin sune kamar haka:

 • WANKA YAYIN TAFIYA


Yana daga cikin sunnar Annabi tsira da aminci su tabbata a gareshi yin wanka kafin tafiya Sallar Idi.

 • CIN ABINCI KAFIN TAFIYA MASALLACI.

Cin abinci kafin ldi koyarwar Manzon Allah SAW ne, ana so mutum yaci abinci kafin zuwa ldi domin koyi da Manzon tsira Allah (SAW).

 • SANYA FARAREN KAYA

Kamar yadda Monzon Allah (SAW) ya sanar da duk wani Musulmi sanya sabbin kaya masu kyau, Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi fari don zuwa sallar Idi.

 • SANYA TURARE.

Yana daga cikin Sunnah kasanya abu mai kamshi a jikin yayin tafiya sallar Idi kamar Turare

 • ZIKITI YAYIN TAFIYA MASALLACIN IDI.


Yana daga cikin sunnar Annabi tsira da aminci su tabbata a gareshi yin Zikiri yayin tafi sallar Idi, kada ya zamana ana tafiya ana zantuka da mutane, zaayi tayin zikirin har Liman yazo.

 • BA’A NAFILA A MASALACIN IDI.


Anaso duk wanda yasamu ikon zuwa masallacin Idi to kadda yayi sallar Nafila domin itama sallar idi din nafila ce kuma sunnah ce.

 • ZUWA MASALACIN IDI A KAFA

Yana daga cikin sunar Ma’aiki (SAW), ga mai tafiya masallacin idi ya tafi a kafa, domin samun laddan taku masu dinbin yawa.

 • CHANJA HANYAR TAFIYA DATA DAWOWA DAGA MASALLACIN IDI.

Wannan koyarwar Manzon Allah (SAW) ne, ba’a son a bi hanya daya. Ana sonmutum ya chanja hanya idan zai dawo daga masallacin ldi.

 • KARANTA

Yana da kyau mutum ya dinga karanta wannan: TAKABBALANNA WAMINA WAMINKUM

 • YIN RAKA’A BIYU A GIDA BAYAN DAWOWA.

Yana da kyau ga wanda yasamu zuwa sallar idi yayi sallah Raka’a biyu bayan dawowa daga Idi.

 • ZIYARA

Yana daga cikin Sunnah Manzon Allah (SAW) yin ziyara bayan kadawo daga masallacin idi.

Masha Allah, Alhamdulillah Allah ya bamu ikon rike wannan bayani kuma yabamu ikon yin amfani dashi amin, Abinda muka fada dai dai ALLAH ya bamu Albarkarsa baki daya abin kuma dabamu fada dai dai ba daga mune Allah ya yafe mana Ami.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »