Wannan kasuwa ta Dawanau, kasuwa ce ta ƙasa-da-ƙasa wacce take a garin Kano.
An kafa wannan kasuwa ta Dawanau a shekarar 1985. Wannan kasuwa an samar da ita ne da nufin rage cunkoso a Kasuwar Sabon Gari .
Wannan kasuwa katafariyar kasuwa ce ta kayan amfanin gona, wacce aka haƙƙaƙe cewa ita ce kasuwar kayayyakin amfanin gona mafi girma a duk faɗin Afirka ta Yamma
KAYAN DA SUKE SAYARWA
Ana sayar da dukkan nau’ukan kayan amfani gona.
Amma an fitar da Zoɓorodo, riɗi, ƙaro, citta, ‘ya’yan tafasa, zogalai, doya, busasshiyar rogo, nau’ukan hatsi (Gero, dawa, maiwa da sauransu), barkono tsidugu, tsamiya, kuka, da sauransu.
ABOKAN HURDA
Zamowar wannan kasuwa babbar kasuwar duniya tana hulɗa da ƙasashen da suka haɗa da Amurka, Jamani, Daular Larabawa (Dubai), Ingila, Saudi Arabia, Indiya, Nijar, Togo, Jamhuriyar Binin (Kwatano), Kamaru, Chadi, Ghana, Burkina Faso, Afirka ta Tsakiya (Central Afrique), Laberiya, Mali, Libiya da sauransu.
Tarihin kano
08027270093