TARIHIN SARKIN KANO IBRAHIM DABO (1819)

0 2,880

Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan Malam Mamuda ya zama Sarkin Kano ne bayan rasuwar Sarki Sulaimanu a ranar Talata 23 / 24th Dhi Qa’ada 1234 AH wanda yay dai dai da  21st Satumba  shekarar 1819.

Tarihi da dama  ya nuna cewa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne ya aiko da wasika yana umartar Jagororin Fulanin Kano da su zauna su shawarta akan yana so ya nada Malam Ibrahim Dabo kanin Malam Jamo na Kabilar Fulani Sullubawa a matsayin Sarkin Kano, to amma su shawarta akan ko ya dace da ya zama Sarkin Kanon. To ance sai wadannan Shugabannin Fulani karkashin jagorancin Malam Jibir na Kabilar Fulani Yolawa suka tattauna kuma suka girmama Sarkin Musulmi Bello ta hanyar yin mubayi’a ga zabin da yayi na Malam Ibrahim Dabo kanin Malam Jamo na Kabilar Sullubawa.

Sai dai an ce wasu yan tsirarin mutane sun ki yarda da zabin. Masana tarihin Kano sun ce Majalisar zaben Sarkin Kano ma ta samo asali ne daga wannan zama da aka yi. Shugabannin wannan zama kuwa sun fito ne daga Manyan Kabilun Fulani kamar haka :

  • Yolawa — wanda daga bisani Sarkin Kano Dabo ya basu sarautar Madaki, kuma suke shugabantar zaman zabar Sarkin Kano har zuwa yau.
  • Jobawa — aka basu sarautar Makama wadda suke rike da ita har zuwa yau
  • Sullubawa — sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta
  • Dambazawa — sarautar Sarkin Bai

Tarihi ya nuna cewa Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya yi fama da matsalar tawaye a farkon mulkin sa, har ta kai yayi yaki mai yawa da yan tawaye.

Babban tawayen da Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya hadu da shi, shine na Sarkin Fulanin Arewacin Kano wato Malam Usman Dantunku na Kabilar Fulani Yarimawa. Ance, shi Malam Usman Dantunku ya kasance shugaban tara haraji na Sarkin Kano a fadin Arewacin Kasar Kano, sannan kuma a wani kaulin na tarihi ance lokacin da Jihadin Shehu Usman Danfodio ya fara, shima Malam Dantunku an bashi tutar Jihadi. Saboda haka ne, bayan Sarki Sulaimanu ya rasu Malam Usman Dantunku yaga cewar to shima fa lokacin sa yayi na cin gashin Kan sa, don haka ne ma sai yaki yiwa Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo mubayi’a.

Masana tarihin Kano, sun ce wannan dalili ne ma ya saka Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya kaddamar da yaki akan Malam Usman Dantunku. Ance an kwashe kimanin kusan shekaru 3 ana gwabzawa tsakanin dakarun Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo da na Sarkin Fulanin Arewacin Kano wato Malam Usman Dantunku. Har wani bature mai yawon neman sanin kasashe dan kasar Ingila wato Hugh Clapperton yaga yadda Malam Usman Dantunku yayi wa mayakan Sarkin Kano Dabo barna. Amma daga bisani Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya samu nasarar fatattakar Malam Usman Dantunku da mutanen sa har zuwa iyaka da Kasar Katsina. Da haka ne Sarkin Kano Dabo ya murkushe barazanar tawayen Dantunku da kuma sauran masu tawaye.

Marubutan tarihin Kano, sun bayyana Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo a matsayin Kasaitaccen Sarki, wanda ya gyra sarautar Kano, kuma yayi tasiri a ciki ta hanyar samarwa tare da jaddada wasu al’adu na kasaita wadanda Kano ce kawai ta kebanta da su. Wadannan al’adu sun hada da :

  • Rike Tagwayen Masu
  • Zama akan karaga, sauran hakimai kuma suna zaune a kasa.
  • Yin nadi mai kunne biyu
  • Saka Takalmi mai Gashin Jimina
  • Samar da Sarautun bayi masu kula da doka da oda kamar su Shamaki, Danrimi, Sallama, Sarkin Dogara, Kasheka, Turakin Soro, Sarkin Hatsi, Kilishi, da sauran su.
  • Banbanta yayan Sarki da na bayi, ta hanyar yi wa yayan bayi tsaga uku-uku a kunchin su.

DOMIN JIN DADIN AIYUKAN KAYI SHARING ZUWA SOCIAL MEDIA DAKE KASA

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »