Furucin Kwaliya A Cikin Hausa Kashi Na Daya

0 369


kwalliya furuci ne don bayyana wani tunani ko wani abu ko wani aiki ta hanyar amfani da wasu kalmomi marasa alaqa da abin da suke bayyanawa” (Mctyre, 2002).

Hassan (2008:40) ya bayyana kwalliya da cewa, “hanya ce ta amfani da wasu kalmomin don bayyana wani tunani wanda ya yi hannun riga da kalmomin”.

(ed) (1983:790) ya bayyana kwalliya da cewa, “adon harshe ne wanda ake fadar wani abu da nufin nuna wani abin daban wanda suke da kamanceceniya”.

Baldick (1990:134) ya bayar da ma’anar kwalliya da cewa, “adon harshe ne mai muhimmanci kuma wanda ya yadu ake bayyana wani aiki ko tunani ta hanyar amfani da wata kalma ko rukunin kalmomi wadanda suke nuna wani abin daban, amma duka biyun suna da alaqa”.

Dangambo (1984:39) ya yi amfani da Kalmar Azanci wajen nuna furucin kwalliya, inda ya ce, “wasu maganganun hikima ne guntaye da akan samu masu kama da Karin Magana. Abin da ya bambanta su da Karin Magana shi ne, saboda ba su da vari biyu. Zance ne a dunqule wanda yake cike da hikima”.

A tawa fahimtar furucin kwalliya wasu jerin kalmomi ne wadanda suke da ma’anarsu amma ake amfani da su wajen bayyana wani abin daban saboda kamancin abubuwan biyu.

Bayanin Wasu Furucin Kwalliya Cikin Rubutun Zube.

Don ganin an fito da yadda bayanin furucin kwalliya yake bayyana cikin rubutun zube na Hausa, a wannan takarda an yi ƙoƙarin ƙago wasu jimloli da suka dace da misalan da aka bayar. Don haka, dukkan misalan da aka bayar ba tsakure bane daga wani littafin zube, ƙirƙira ce ta marubucin wannan takarda.

  1. Gudun Tatsattsiyar Akuya

A zahirance wadannan kalmomi suna nufin gudun da akuya take yi ana sakinta bayan an gama tatsar nononta, amma a kwalliya maganar na nufin mutum ya guje wa wani abu bayan abin ya rigaya ya faru. Misali cikin rubutun zube:

“… a lokacin da suke zaman daduro, Kande ba ta gane ba, sai bayan ta tafi gida sannan ta gane ta yi gudun tatsattsiyar akuya, don kuwa tana dauke da cutar qanjamau”.

  1. Zaman ‘Yan Marina

A zahiri wadannan kalmomi suna bayyana yadda marina suke zama a marina yayin da suke aikin rini, amma a furucin kwalliya kuwa, maganar na nufin kowa da inda ya nufa a zamantakewa.

Misali cikin Rubutu Zube: 

“… tun lokacin da aka daura auren Mati da Dela suke zaman ‘yan marina kasancewar ba sa son junansu aka daura auren”.

  1. Shan Kunun Ganga

Ganga tana nufin gava ko gaci. A zahiri wadannan kalmomi suna bayyana yadda mashaya kunu suke shansa, musamman idan mai zafi ne, wato su dinga yadar gefe-gefe, amma a furucin kwalliya maganar na nufin raragefe ke nan.

Misali cikin Rubutun Zube:

“…tun lokacin da Nasir ya ƙyalla ido ya ga yarinyar nan, sai ya fara shan kunun ganga ta yadda zai yi mata magana domin kuwa ya ji cewar yarinya ce mai izza”.

  1. Kama ƙafar Wala

Wala wata tsuntsuwa ce mai siririyar qafa. A zahiri wadannan kalmomi suna nuni ne da kama ƙafar wannan tsuntsuwa, amma a furucin kwalliya ana nufin mutum ya bi hanyar da ba za ta ville da shi ba.

Misali cikin Rubutun Zube:

“… ganin yadda Hafsa take kyautata masa, sai ya zaci sonsa take yi, don haka sai ya kama ƙafar wala ya saki matarsa Kande”

  1. Kafircin Mage

A zahiri kalmomin suna bayyana tunanin Bahaushe game da al’adar mage yadda take shasshafa kafafunta da fuska kamar tana alwala, amma ba a taba ganin ta yi sallah ba, amma a furucin kwalliya maganar na nufin yaudara ke nan.

Misali cikin Rubutun Zube:

“…Haqiqa Jummai ba ta ƙaunar Ado, amma ta ƙi bayyana masa, tana ta yin kafircin mage tana karbar abin hannunsa”.

Marubuci: Tijjani shehu almajiri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »