JIGON FADAKARWA DA BAN DARIYA CIKIN WAKOKIN TASHE 2

0 914

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A Jigon Fadakarwa Da Ban Dariya Cikin Wakokin Tashe 1️⃣ munyi bayanin Jigon Fadakarawa Cikin Wakokin Tashe don haka yanxu zamuyi bayani Akan JIGON BAN-DARIYA A WAKOKIN TASHE

JIGON BAN-DARIYA A WAKOKIN TASHE

Ban-dariya hanya ce da ake amfani da ita wajen sanya mutane su yi dariya da walwala da kuma nishadi wanda kuma ake isar musu da wani darasi ta hanyar dabara.

Bargery (1934:76) ya bayyana cewa, ban-dariya ta samo asali ne daga kalmar ‘bandare’ wadda take nufin, mutum mai bayar da dariya ko mai sa a yi dariya.

Shi kuma Ibrahim (1976:104) ya bayyana ban-dariya da irin wakokin da ‘yan gambara da ‘yan kama da ‘yan galura da ‘yan koroso suke yi. dangambo (1982:1) ya bayyana ban-dariya da fada ko yin abin da za a yi raha, a kyalkyala, a yi shewa ko akalla a yi murmushi.

A wakokin tashe, ana amfani da ban-dariya wajen isar da sako ta hanyar wasa wadda mutane suke koyar wani darasi ta hanyar nishadi. Misalan wakokin tashe masu jigon ban-dariya sun hada da:

dan bera mai shiga rami,
Amshi: In na shiga kar ku jawo ni.

Wannan waka tsagwaron ban-dariya da nishadantarwa ta kunsa, kasancewar kuma ana rera wakar, shi kuma wanda aka daurawa yana kokarin cusa kansa cikin wani lungu, ragowar kuma na kokarin jawo shi.

Abubuwan da yara sukan yi amfani da su a wannan wasa, ba sa wuce hoda ko farar kasa ko bula wadda suke shafawa a fuskokinsu, sai igiya wadda ake daura wa wanda suka zaba a matsayin dan beran.

Mai kiriniya,
Amshi: Iye.
Wa ya sa ka ne?
Amshi: Oho!

Wannan wakar tashe da tashen kansa, cike yake da ban-dariya da annashuwa. Wannan wakar tattare take da ban- sha’awa ta yadda mutanen gidan kan kasance cikin raha da annashuwa.

A nan ma, abubuwan da yaran suke amfani da su, su ne; hoda ko farar kasa ko bula, sai kuma igiya wadda ake daura wa mai kiriniyar. Suna aiwatar da tashen ne ta yadda wanda aka daurawa zai dinga tabe-taben abubuwa a inda suke aiwatar da wasan.

‘Yan mata a daina bilicin,

Amshi: Kun ga abin da bilicin yai min.

Wannan ma wakar tashe ce da take kunshe da ban-dariya, kasancewar yadda wadda ta yi bilicin din take aiwatar da tashen da wakar. Yara mata ne suke aiwatar da wannan tashe ta hanyar tanadar abubuwa kamar; jar hoda ko jan zabibi, sai a sami daya daga cikinsu a shafa mata a fuska ya ji sosai.

A yayin aiwatar da tashen kuma, wadda aka shafawa tana ‘yar rawa tana nuna fuskarta, ragowar kuma suna maimaita amshin; “Yan mata a daina bilicin”.

      dan tsoho ga mutuwa nan,

Amshi: Ku gaya mata ban shirya ba.
dan tsoho ga mutuwa nan,
Amshi: Sai na ci tuwo na koshi.

Wannan wakar tashe ma cike take da ban-dariya da sanya annashuwa ga masu kallo, tattare da yadda tsohon yake aiwatar da tashen. Wannan tashe yara maza ne suke aiwatar da shi, sannan sukan zabo wanda ba shi da kiba sosai a cikinsu ya sanya babbar riga, kuma ya dinga rawa yana rausaya kamar tsoho, yana wakar su kuma suna amsawa.

     Ni ne bakin birin nan da ake fadi,

Amshi: Tababbe.
Ba ga ni ba,
Amshi: Tababbe.
A taba ni man,
Amshi: Tababbe.

Wannan wakar tashe ce da ake aiwatarwa cikin tashe domin nishadantarwa da ban-dariya ga masu kallo. Yara maza ne suke aiwatar da shi ta hanyar tanadar farar kasa ko hoda ko bula domin shasshafawa a fuskokinsu. Haka nan, daya daga cikinsu zai tube rigarsa ya shafe jikinsa da farar kasar ko bula ya rike itace , su kuma ragowar su daura masa igiya a kugu, suna tafe suna wakar shi kuma yana zazzare ido yana kokarin kai duka.

       Ya ci buhun dawa,

Amshi: Joji Bush.
Ya ci buhun masara,
Amshi: Joji Bush.
Mai katon ciki,
Amshi: Joji Bush.

Wannan waka ce da ake aiwatarwa a cikin tashe wadda ta kunshi ban-dariya da nishadantar da masu kallo. Yadda ake aiwatar da tashen tattare da yadda ake rera wakar suna kara samar da raha ga mutane.

Yara sukan zabi mai kiba a cikinsu sai kuma su tanadi tsummokara ko kwarya domin wanda aka daurawa tashen ya sa a cikinsa domin cikin ya yi kato. Daga nan, sai su shasshafa farar kasa a fuskokinsu, duk inda suka je don aiwatar da wasan, sai ya zauna shirim, su kuma sauran suna yin wakar.

Zan buge,
Amshi: kar ka buge birin Kano azumi ne.
Zan buge,
Amshi: kar ka buge birin Kano sai hakuri.

Wannan waka ce da ake aiwatarwa cikin tashe mai kunshe da ban-dariya. Yanayin yadda ake aiwatar da tashen, da kuma yanayin wakar suna bayar da raha da annashuwa ga masu sauraro. Kamar tashen bakin biri, wannan ma yara maza ne suke zabar daya daga cikinsu su daura masa igiya a kugunsa, shi kuma ya rike katon itace yana zazzare ido yana kai duka a duk inda suke aiwatar da wasan, shi kuma mai rike da igiyar yana jawo shi baya, sauran kuma suna ba shi hakuri.

KAMMALAWA

Wannan takarda ta kunshi bayanai kan ire-iren jigogin da ake samu a cikin wakokin tashe. A ciki an yi kebabben nazari a kan jigogi guda biyu. Akwai jigon fadakarwa da kuma jigon ban-dariya. A ciki an yi kokarin kawo wasu wakokin tashe wadanda suke fadakarwa a kan fannonin rayuwa daban-daban. Haka kuma, an yi kokarin kawo misalai da bayanan wasu wakokin da suke kunshe da jigon ban-dariya.

A wajen masu yin tashe da masu kallo, ban-dariya da kawo nishadi su ne manyan manufofinsu amma a zahiri akwai wasu manufofin da yawa, kamar fadakarwa da sauransu.

MANAZARTA

Alhamdu, I.D.(1973) Tashe Musamman na kasar Kano, Report on Summer
Project, Kano: ABC,ABU.

Bargery, G.P.(1934) Hausa-English Dictionary and English-Hausa bocabulary,
London: Odford Unibersity Press.

Buhari, M.(1988) “Nazarin Jigon Wasu kagaggun Labarai na Hausa” Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Chamo, I.Y. (2006) Sako a Finafinan Hausa:Nazari a kan Jigo da Rabe-rabensa.
Kundin Digiri na Biyu, Kano: Jami’ar Bayero.

dangambo,A.(1981) “daurayar Gadon Fede Waka” Kano: Sashen Koyar da
Harasunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

dangambo, A.(1982) “Jigon Bandariya a Adabin Hausa” Departmental Seminar.
Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

dangambo, Halima,A.(2002) “Salon Sarrafa Jigo a Adabin Baka na Hausa: Nazari
Kan Jigon Fadakarwa, Kundin Digiri na daya, Kano: Jami’ar Bayero.

East,R.M. da Wasu (1948) Zaman Mutum da Sana’arsa, Zariya: NNPC

Gusau, S.M.(1983) “Wakokin Noma na Baka: Yanaye-yanayensu da Sigoginsa” a
cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, bol.1 No.1
Kano: Bayero Unibersity.

karaye, M. (1970) Tashe By Male People, Report on Summer Project, Kano:
ABC,ABU.

Mukhtar,I (2002) Jagoran Nazarin kagaggun Labarai, Kano: Joji Publishers

Umar, M.B.(1981) Wasannin Tashe, Zaria: NNPC

Yahaya, I.Y (1978) “Nazari Kan Yanayin Wasan Kwaikwayo na Hausa, Takardar
da ya gabatar a taro kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar bayero.

‘Yar’aduwa, T.M.(2001) “Wasan Kwaikwayo: Sigoginsa da Jigoginsa” a cikin
Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies bol.1. No.1. Kano:
Bayero Unibersity.

Daga
Tijjani Shehu Almajir


Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »