Tarihin Birnin Maiduguri
GABATARWA:
Garin Maiduguri dai ita ce babban birnin jihar Borno dake yankin arewa maso gabas shin Najeria. Maiduguri ita ce birnin da tafi kowane birni girma da fadin kasa da kuma yawan jama’a a arewa maso gabas shin Najeriya.
Akalla birnin tana da jama’a fiye da miliyan daya. Birnin Maiduguri da sabon birni ne kuma an kafa shi a shekaran alif da dari tara da bakwai (wato 1907). Maiduguri ya kunshi unguwar Yerwa (Yerwa yana nufin alheri a harshen kanuri) ta yamma da kuma tsohuwar Maiduwuri ta bangaren gabas.
Mulkin Birnin Maiduguri shi ne fadar mai martaba shehun Borno kuma ita ce fadar gwamnatin jihar Borno.
KASUWANCI DA TATTALIN ARZIKI
Babban kasuwan Maiduguri ita ce kasuwar litinin wadda take a tsakiyar birnin Maiduguri (Monday Market). Abubawan cinikayya sun hada da tufafi, kayan masarufi, kayan abinci, tukwane, bangaren motoci da babura, kasets na CD da DVD, telebijin, rediyo, takalma da sauransu.
Kananan kasuwanni a Maiduguri sun hada da kasuwan Kwastam (Custom) wanda yake tsakanin unguwar Gamboru da Gwange, kasuwar Budum, kasuwar tashan Baga wanda ya yi suna wurin cinikayyan kifi da ake kowowa a garin Baga wanda yake dab da tafkin Chadi.
Yawancin mutanen garin Maiduguri dai manoma ne amma akwai ‘yan kasuwa da dama da kuma ma’aikatan gwamnati.
Manyan masana’antun Maiduguri sun hada da Maiduguri Flour Mills, kamfanin sarrafa Dalaram (wanda a halin yanzu ta dur’kushe), kamfanin Coca-Cola, Borno Aluminium company, Kamfanin Alewa ta Haske da kuma kamfanin sarrafa takalma ta Natel. Akwai bankuna da yawa a Maiduguri a kan titin Shehu Laminu Way.Yawancin bankuna suna da daukan ku’di da kanka wato ATM.
ZIRGA-ZIRGA
Maiduguri tana da filin jirgin sama wadda ake kira da sunan Maiduguri InternationalAirport.
Jiragen sama kan tashi kowane rana daga Maiduguri zuwa Abuja da Lagos. D.s akwai kuma jiragen da suke zirga-zirgan daukan Musulmai zuwa Saudi Arabia lokacin aikin Hajji.
Ta fannin jiragen ‘kasa kuwa Maiguri tana da Makeken tashan jirgin kasa wanda aka fi sani da Railway Terminus Maiduguri.
Tashan jirgin kasan tana dab da inda rikicin Boko Hram ya Barke a shekarar 2009 a unguwar Goni Damgari bayan kwatas. Daukan shanu daga Maiduguri zuwa kudancin Najeriya yana daya daga cikin manyan dilalan kafa layin jirgin kasa aMaiduguri.
Maiduguri tana da manyan titunan mota kamar su Sir Kashim Ibrahim Road, Shehu Laminu Way, Bama Road, Jos Road da Baga Road, da kuma Dambo’a Road. Hanyoyin motan sun hada Maiduguri da sauran birane kamar Yola, Kano da Bauchi.
Akwai kuma hanyoyi zuwa kasashen waje kamar Chadi, Nijar da Kamaru.
ILMI DA MAKARANTU
Makarantunda dake cikin kwaryar birnin Maiduguri sun hada da babbar jami’ar nan mai farin jini wato jami’ar Maiduguri wanda ake kira da sunan (University of Maiduguri). Jami’an yana kan hanyar Bama Road daura da gidajen (303 Housing Estate).
Kwasa-kwasai {Cources} da ake karantarwa a jami’ar sun hada da ilmin aikin likita, ilmin injiniya, ilmin koyon aikin jarida, ilmin harshen turanci da kuma ilmin addini da al’adu. Jami’ar Maiduguri tana da Asibitin koyarwa na ”Univesity of Maiduguri Teaching Hospital”. Sa’annan akwai makarantar politeknik a Maiduguri mai Suna Ramat Polytechnic.
Sauran Makarantun zirfin ilmi sun hada da College of Agriculture, dake daura da (505 Estate Housing) Sir Kashim College of Education, da Mohammed Goni College of Islamic and Legal Studies. Sa’annan akwai makarantun sakandare da dama a Maiduguri.
MASAUKIN BA’KI
Wuraren saukan ba’ki a Maiduguri sun hada da Lake Chad Hotel, Dujima Hotel, Deribe Hotel, Ali Chaman Guest Inn da kuma Maiduguri International Hotel. Nishadi da Wuraren Bude idon Ba’ki a Maiduguri su kan iya ziyartan makeken kasuwan litinin, fadan mai girma shehun Borno da kuma gidan dabbobi Zoo na Sanda Kyarimi Park wanda yake tsakiyar birni Maiduguri.
ADDINI
Yawancin mazauna birnin Maiduguri dai Musulmai ne. Amma akwai mabiya addinin kirista da dama a garin. Kana akwai manyan majami’o’i da dama a garin kamar babban majami’an dake kan titin Kiri Kasamma.
Maiduguri ya yi suna kwarai wajen karatun alkur’ani a inda dalibai daga dukkan fadin Najeriya suke zuwa garin domin neman ilmi. Manyan masallatai a garin sun hada da masallachin Mai Deribe, masallacin Madinatu, Masallacin Kofar Shehu, Masallacin Indimi da ke titin Dambo’a, Masallacin Sheikh Ibrahim Saleh Al’hussain. Akwai shahararrun malaman addinin Musulunci da dama a birnin Maiduguri wadanda za ba su kirgu ba.
A shekarar 2009 ne, wani malamin addinin Muslunci wanda aka fi sani da sunan Mallam Muhammad Yusuf ya kyan -kyashe kasa a garin in da yake ikirarin ya’ki da gwamnati da kuma ilmin Boko wanda a ganinsa yana lalata tarbiyyar al’umma ne mussamman ‘ya’ya mata. Sa’adda aka yi kimanin mako guda ana fgwabzawa tsakanin sojoji da ‘yan sanda da kuma magoya bayan Muhammad Yusuf. Wannan tarzoma ta zame sanadiyyar rasa rayukan al’umma da dama a jihar Borno.
Daga karshe jami’an tsaron gwamnati su kayi nasarar cafke Muhammad Yusuf. “Major General Hassan Kaoje” ne ya cefke kuma ya dan’ka Yusuf a hannun ‘yan sandan.
Wata rana da misalain karfe 05:30pm labarin kisan Muhammad Yusuf ya yadu a jihar Borno. ‘yan sanda sun yi ikirarin cewa ya rasu ne a ya yin da aka bindige shi lokacin da yake kokarin kubucewa
Daga Adamu Aliyu Ngulde