An haifi Aisha Halilu ran 17 ga watan Fabrairun 1971 a jihar Adamawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Kakanta Alhaji Muhammadu Ribadu shi ne ministan tsaron Najeriya na farko.
Ta yi digirinta na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin Public Admimistration, sai ta yi digirinta na biyu a kan harkokin kasashen waje.
Ta yi difloma a fannin kwalliya a makarantar koyon ado ta Carlton Institute da ke Windsor a Birtaniya, da kuma wata makarantar koyon gyaran jiki ta Academy Esthetique da ke Faransa.
Kafin maigidanta ya zama Shugaban Najeriya, tana da shagon gyaran jiki da kwalliya mai suna Hanzy Spa a jihar Kaduna.
Ta wallafa wani littafi na koyar da kwalliya da gyaran jiki wanda Hukumar da ke kula ta makarantun kimiyya da fasaha ta Najeriya ta sa shi a cikin manhajar da makarantun za su yi amfani da shi.
Aisha ta auri Muhammadu Buhari tamda shekara 18 kuma itace matarsa ta biyu ta haifi ‘ya’ya biyar da Muhammadu Buhari.
- Aisha Buhari
- Halima Buhari
- Yusuf Buhari
- Zarah Buhari
- Amina Buhari
Yusuf Buhari Zahra Buhari Halima Buhari Hanan Buhari