YADDA ZAKI SHIRYA MIYAR EGUSI

0 2,403

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Miyar egusi miya ce dake daukar hankalin maigida matsawar kin tsaya kin shiryata kamar yadda na rubuta ina fata zakiyi kokarin bin yadda abin yake don ki kwadaitawa magidanki miyar egusi

ABIN BUKATA.

 1. Egusi
 2. Ugo leave
 3. Stock fish
 4. Bushashen kifi
 5. Ganda
 6. Cubes Maggi
 7. Manja
 8. Attaruhu
 9. Albasa
 10. Naman saniya
 11. Daddawa cokalin shayi 1-2.
 12. Spices kadan

YADDA ZAKI HADA TA.


Na jajjaga attaruhu na da albasa guri daya nasa manja a wuta yayi zafi sai na zuba attaruhu da albasa da dan daddawa.

Asoyasu kadan sai na kawo egusi na xuba a ciki na cigaba da juyashi occasionally har sai da manja ya ratso jikin egusi din sai na kawo ruwan tafashen nama na xuba na juyashi sosai sai na rufe.

Dama kin wanke gandarki ki dan dafata tayi laushi.

Sai ki bude tukunyarki sai ki zuba gandar ki kara ruwan zafi ki juya ki rufe bayan wasu mintina sai kisa naman shanu dinki wato sai ki juya bayan minti kadan sai kisa stock fish da dried fish dinki ki juya ki rufe ki barshi y kara dahuwa sai kisa Magi cubes da bushashan kifi dinki dakakke ki juya sosai ki rufe xaki iya kara dafaffen ruwa kadan sai ki rufe ki barshi for some minutes sai kisa spices dinki ki Kawo ugu leaves dinki da kika wanke kika tsane ki zuba ki barshi kamar 5 minutes sai ki sauke.

Nikam idan nayi nakanci kayana da kowanne irin nau’I na tuwa, kema zaki iya gwadawa. Aci dadi lafiya.

Masha Allah Kitura zuwa wasu Groups don Karamin Kwarin Gwiwa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »