YADDA ZAKI HADA MIYAR OGNO

0 655

KAYAN HADI

  • Nama
  • Kifi danye da busasshe 
  • Ogbono 
  • Ganda 
  • Kayan miya
  • Man ja 
  • Maggi da gishiri 
  • Curry da tafarnuwa

YADDA ZAKI HADA:

Ki tafasa namanki da gishiri, tafarnuwa, albasa, ki soya man ja amma kadan, ki zuba markadadden kayan miyarki a kai, su ma ba da yawa ba, idan ya soyu sai ki zuba dakakken crayfish kamar cokali biyu, ki zuba busasshen kifinki da kika gyara, ki zuba ruwa a kai, idan ta dahu sai kisa baking powder kadan dan tayi yauki sosai, dama kin sulala danyen kifi kin bare, kin cire kayar, kin gutsuttsura, shi ma sai ki zuba, ki rufe zuwa minti biyar ko goma shike nan kingama miyarki.

Allah yabada ikon ci lafiya kuma kiturawa wasu yan Uwan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »