SAUSAGE ROLLS
- Nama
- Kwai
- Busassan Buredi
- Albasa
- Magi
- Attaruhu
- Gishiri
Zamu nuke danyan nama ko mu dake ya daku sosai, albasa mu yayyankata da attaruhu sai mu barbada magi da gishiri da korin mu fasa kwai,mu hada komai da komai waje daya saimu nannade naman a barbadeshi da garin buredi zamu shafa mai a farantin mu gasa naman acikin oven wato baking tray mu dora naman nan da muka hada mu saka a oven, don gasuwa