GINSHIKIN DIMOKURADIYYAR CIKIN GIDA

0 264

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dimokuradiyyar cikin gida (ko internal democracy, a Turance) wata kalma ce da yawancin masu goyon bayan jam’iyyun siyasa ke kafa hujja da ita don bayyana adalci ko zaluncin shugabanninsu.

A kwatance mafi sauki, wannan kalma na magana ne bisa wajabcin girmama zabin ’yan jam’iyya da mutunta su, ta fuskokin ba su damar darje mutumin da suke son ya wakilce su, ko ya shugabanci wasu al’amuran da suka shafe su, a siyasance ko a gwamnatance.

Har ila yau, kalmar na nuni da bukatar samun shugabanci mai waiwaye da tuntubar jama’a cikin gabatar da ayyukansu. A takaice, dimokuradiyyar cikin gida na nufin duk dabarun da bin su zai tabbatar ba a yi wa mabiya hawan kawara ba.

Dimokuradiyyar cikin gida wata aba ce da ake gina ta bisa wani muhimmin ginshikin da ya shafi yanayin rayuwar mutane kamar su: Iliminsu, Tattalin Arzikinsu, Al’adunsu, Akidarsu, Tarihinsu, Bukatunsu, dalilan kafa Jam’iyyunsu da kuma yunkurin kyautata Makomarsu.

Da farko ya kamata mu fahimci falsafar siyasa, wadda ta fuskarta aka samu hanyoyin kafa jam’iyyu don a yi gasar neman jagoranci, ko mulki, ko shugabancin al’uma, ba wata aba ce da nishadi, ko mafarki, ko tsautsayi, ko tsintuwa ta samar da kasancewarta ba. Gaggan malaman duniya na daulolin da suka rayu na dauri, su suka samar da koyarwar irin wadannan falsafofin.

Tarihin haihuwar dauloli, kalubalen da rayuwarsu ta yi gwagwarmaya da shi, addinansu, da sauran akidu suna da kaso mai tsoka wajen tsara yanayin falsafar siyasar al’uma na kowane karni. Akwai malaman falsafar da suka kalli rayuwa da tabaron addini, wasu da na tattalin arziki, wasu da na al’ada, wasu da na tsabagen gwagwarmayar jinsuna da dai sauransu.

Daya daga dalilan da suka sa wani sashi na Musulmi ke kalubalantar tsarin dimokuradiyya da akidarta shi ne, kasancewar falsafar ta samo asali daga koyarwar addinin Kirista wanda ya rarrabe tsakanin bikin duniya da bikin lahira.

A Musulunci duniya gona ce da mutane suke ta aikin shuke-shuke, lahira kuma, a can ne ake girbar duk irin abin da mutum ya shukan. Don haka, mutum ya dauka akwai wasu sabgogin da suka jibinci addini, akwai kuma wadanda ba ruwan addini da su, sakarci ne.

Ba magana za mu yi game da cancantar shiga harkokin dimokuradiyya ko wajabcin kaurace musu ba. Kasancewar lalular zaman Nijeriya, a yadda take, ta dire mana dutsen dimokuradiyya a gabanmu, ana so ne a yi magana game da ginshikin da wasu al’umomi ko kasashe suka gini dimokuradiyyar cikin gida a kansa.

A batu na gaskiya, kwamacalar da shugabanni ke yi a kasashenmu masu koma baya, ta sa mutane da yawa tunanin cewa tsarin dimokuradiyya bai dace da mu ba. Dimokuradiyya tsari ne da yake bukatar koshin abinci, yalwatar ilimi, samun wayewar talakawa, kubuta daga kangin talauci, da kuma tsayuwar doka da oda a kasa. Idan daya daga wadannan muhimman abubuwa suka samu cikas, da wahala dimokuradiyya ta inganta.

Dimokuradiyyar cikin gida, a matsayin bai wa mutane ’yancin zabin abubuwan da suka dace da su, ba ta inganta har sai mutanen sun san kansu yadda ya kamata. Mutumin da bai mallaki abincinsa ba, ba shi da kowanne nau’in ilimi, bai wuce hukuma ta keta shi don cin zali ba, bai san me al’uma ke ciki ko fuskanta ba, ta fuskoki da dama, bai halasta jam’iyyarsa ta yi masa siddabarun cewa yana da cikakken ’yancin zabi ba. Saboda ko ya zaban, bai san me ya zaba ba!

A tarihin siyasar kasar nan, jam’iyyun da Yarbawa suka kafa sun fi sauran jam’iyyu tsayawa don sauke alhakin yi wa talakawansu jagoranci don kar su yi zaben tumun dare. Misali, tun daga lokacin sayen fom din “na-gani-ina-so” , jam’iyyun AG da UPN da AD da AC da ACN suke tabbatar da cewa duk mutumin da cancantarsa ba ta kai ya tsayawa jam’iyya ba, an tankade shi, an rairaye, an watsar gefe.

Wannan ba zai samu ba sai jam’iyya na da akida da manufa da alkiblar da take son al’umarta su fuskanta don cim ma wani dunkulallen burin kyautata gobenta.

Ba mutumin da bai da amfani a jam’iyya. Duk da haka, kowa akwai irin abin da ya fi dacewa da shi. Misali, ba don Ahmed Bola Tinubu ya yi tsayin daka sai Fashola ya gaje shi ba, da an saki filin sukuwar dimokuradiyyar cikin gida babu ka’idar cicciba cancanta da caccake cuwa-cuwar cuce-cuce, da yau watakila wani lalatacce ke gwamna a jihar Legas.

Bai wa makafi damar zabin kalar da kowannensu ya ke sha’awa ba adalci ba ne, yaudara ce. Goyon bayan saurayi maras mazakuta, a neman auren gansamemiyar budurwa, ya fi kama da zawarcin masifa da rana tsaka. Idan yaro na neman hadiye gatari, rashin imani ne manya su sakar masa kota.

Watakila mutanen da suka san tarihin ayyukana na siyasa da kuma irin kungiyoyi da jam’iyyun siyasar da na taba shiga, su yi mamakin bayanina na son yi wa dimokuradiyyar cikin gida kundumi, ko kadan ba haka bane. A duk fannonin rayuwa, akwai farillai, da sunnoni, da mustahabai da sauransu. Samun nagartaccen shugabanci, halastacce, mai kishin jama’a, mai amana da ma’ana da amfani ga rayuwar al’uma, shi ne gaba da wangame kofofin jam’iyyu, babu ka’idar tabbatar da irin mutanen da suka cancanta su shiga zabe da sunan wakilcin jama’a.

Koke-koken da mutane ke yi, na raunin arewa a siyasar Nijeriya ta yau, sun samu ne saboda yawancin masu wakilcin jam’iyyun siyasa daga arewa, a matakan mulki daban-daban, ba su cancanci wakilci ba.

Kashi casa’in da biyar na wakilanmu a majalisun tarayya sun gaza wakilan sauran sassan kasar nan kamala da ilimi da gogewa da sanin makama da cancantar wakilci. Me ya kawo haka? Sangartacciyar dimokuradiyyar cikin gida, kamar yadda muggan shugabanni suke sarrafa akalarta.

Yawancin mutanen da ake taimakawa shiga takara da cin zabe, mutane ne masu rauni, wadanda ba za su iya kallon kuda da shugansu ba, balle su tilasta shi ya aikata alheri.

Sau da yawa shugabannin jam’iyyun siyasa sun fi sha’awar tsayar da yaransu, masu kula da kamfanoninsu, ko gonakinsu, ko wasu kadarorinsu takarar wakilcin al’uma. Ta haka wasu barori suka cim ma nasarar hawa kujerun gwamna a arewa. A halin da arewa take ciki wannan ba zai haifar mana da da mai ido ba.

Idan al’umar arewa ya kasance tana da wani abu da take son cim ma, a yau-yau ko a gobe, tilas ta sake tsarin hanyoyin da ’yan takararta za su dinga fitowa daga jam’iyyun siyasar da ake da su.

A kudu, mafiya yawan masu tsaya musu takarkaru sun cancanta bisa yanayin al’umarsu. Dawakan kilisa ba da su ake wasan polo ba! Babbar masifar da ke damun mutanen arewa ta fuskar siyasa, ba kamar rikon-sakainar-kashin da ake yi wa harkar samuwar shugabanni ta fuskar zabe. Da ba haka abubuwa suke ba.

Shugabannin jam’iyyu a wuyansu alhakin samuwar nagartaccen wakilci, a kowane mataki, ya rataya. Don haka wajibi ne a kansu su tabbatar mutane baragurbi ba su sami damar wakilcin al’uma ba.

Mutane jam’iyyu suke zaba don akidunsu da tarihinsu da gogaiyarsu. Cin amana ne shugabanni su yi biris da harkar wace hanya za a bi halastaccen wakilci ya samu. Duk da lalacewar abubuwa a arewa, har yau muna da sinadarin wakilai da sanatoci da tsirarun gwamnoni masu bayar da nagartaccen wakilci ga al’umarsu.

Idan yawan dukiya da kwarewa a harkar ta’addanci da sanin makirci suka zama dalilan samun damar tsayawa wakilci, kowa ya kuka da kansa. Mutanen kudu ba su fi mu komai ba sai iya tsari. A kudu, al’uma da kungiyoyin kwararru, da na sana’a, da na al’adu, da na addinai ke darje irin wakilan da ya kamata su wakilce su. Wannan ne yake wajabta kowane bangaren al’uma aiko da nagartattun wakilai.

A arewa, tsayawa takara daidai take da neman aure. Kowa kansa yake fitowa. Kowa kansa yake wakilta. Ba ruwan kowa da tsayawarka, sai ka ci zabe. Ta yaya wakilanmu za su kulla abin arziki duk kyawun niyyarsu? Sai kalilan!

Daga: Dakta Auwalu Anwar

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »