Yadda Uwar Gida Zata Dafa Coconut Rice (Shinkafar Kwakwa)

0 999

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yadda Zaki Dafa Shinkafar KwaKwa.

Shinkafar Kwakwa shinkafa ce ake Dafawa kusan kamar yadda ake dafa dafadika, amma a wajen kayan hadin a nanne wasu abubuwa ke canzawa.

Shinkafar kwakwa nada dadi matukar gaske domin matuƙar mai gidanki yaci to zaiso ki ake Dafadika a gefe ki dinga yi masa irin wannan domin tafi daɗi ga kuma da ɗin ƙamshi a yaci.

Wanda hakan kan sanya mai gida yaci dayawa baimasan yaci ba.

Kadda mucika uwar gida da yan mata da surrutu cikin sauri kayan da zaki nema wajen yin sune:

  • Shinkafa,
  • Kwakwa ƙwallon 3,
  • Koren Tattasai,
  • Jan Tattasai,
  • Tafarnuwa,
  • Danyar Citta,
  • Albasa,
  • Crayfish,
  • Man gyaɗa ko Man kwakwa,
  • Kayan ɗanɗano (Su Magi su gishiri da sauran su).

Zaki iya ƙarawa da (Ba dole bane amfani da su):

  • Onion Powder (Garin Albasa),
  • Cayenne pepper (Garin Yaji) 🌶️,
  • Yellow Pepper,
  • Dried thyme,
  • Paparika (Garin Tattasai),
  • Garlic Powder (Garin Tafarnuwa),
  • Ground Black Pepper

Yadda Za’a Hada.

Mataki Na Daya

Da farko uwar gida zata fara wanke shinkafar ta sosai ta wanko saita zuba a kwadon tsanewa don ta tsane sosai.

Mataki Na Biyu.

Kafin tsanewar shinkafar ki, saiki ɗauki kwakwa ɗinkin saiki fasata kicire bawan nata.

Coconut rice
Yadda Zaki yanka kwakwar ki kafinnikawa

Saiki samu ƙaramar wuka kidan yayyanka ta yadda zakiji dadin niƙata a blender ko dakawa a ƙaramin turmin ƙarfe.

Bayan kin daka ko kinyi blending dinta saiki tace ta a wani kofi mai kyau ki ajiye a gefe.

Mataki na Uku;
Zaki yayyanka attaruhun ki ko kuma Tattasai ɗinki, Citta da sauran su.

Uwar gida zata ɗauko kayan haɗin ta, irinsu man gyaɗa ko man kwakwa, koren Tattasai, jan Tattasai albasa, Citta, tafarnuwa, sai kuma kayan ɗan ɗanonki wato Magi gishiri da sauran su theme, duk saiki zuba a tukunya saiki kawo ruwan kwakwa ɗinki da kika ajiye saiki zuba a ciki.

Idan sun tafasa saiki kawo shinkafar ki da kika wanke saiki zuba ta a ciki ki rufe idan ta kusa dahuwa saiki kawo crayfish ki zuba kadda kusa crayfish din da yawa saboda zai kawar da ƙamshin kwakwar.
Haka kuma zaki kawo kwakwar da kika dan yanka ƙanana ƙanana sai ki zuba a kai kamar yadda kika zuba crayfish ɗinki.

Ki rufe zuwa wani dan lokaci saiki sauke.

Shike nan shinkafar kwakwa ta gamu sai ci.

Coconut rice
Dafafiyar coconut rice

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »