TARIHIN BARBUSHE DA TSUNBURBURA

0 6,672

Barbushe, wani shahararren mafarauci ne da masana tarihi suka ce shi ne mutum na farko da ya hada kauyukan a karkashin ikonsa a lokaci guda. Ya kuma kafa shugabancin Kano baki daya.

Barbushe mutum ne kato,kakkarfa mai tsananin gizo da gashin baki, yakan sanya warki, ya timee kulki a hannun sa. Yana iya kashe giwa ya dauke ta yayi tafiyar wuni guda da ita . Gidan sa yana kan Dutsen Dala inda wani gunki yake Wanda jama’ar ke Bautawa mai suna tsunburbura yana cikin wata kewayayyiyar bukka wada suke kiranta Shamus.

Barbushe shine sarkin fadar tsumburbura, Shine tamakar wakilin wannan Gunkin wanda aikin sa shine kula da jama’ar dake bautawa wannan tsafin.da yake barbushe ne kadai keda izinin shiga wajen tsumburbura, shi yake karbo sakon shekara daga wajen tsumburbura ya fadawa mutanensa, yana da fadawa kamar su Tunzagu, mai gida a gidin gwauran Dutse daga gabas akwai kuma Danbury mai Gida a jigirya da Jandamisa mai gida a magwan Hambarau mai gida Tanagar da kuma Gumbari jadu a fanisau da wadansu da yawa wajen dutsen Danbakoshi da Dankwai.

Barbushe akan Dutsen Dala yake,baya saukowa sai shekara shekara. Idan lokacin saukowar sa yayi sai mutanen nahiyoyi da fadawan nan nasa suke ,su hadu a gidin Dutsen Dala.

Su kanzo tare da abin hadayarsu ga gunki tsunburbura, kamar su Bakaken Bunsurai , Bakaken karnuka da kuma bakaken Kaji wadanda zasu yankawa gunki, Idan an gama basu labarin shekara.

Da zarar almuru (Magariba) tayi sai barbushe ya gangaro sai makada su fara kida, shi kuma sai yayi ihu yayi karaji sannan yayi wasu kalmomin tsafi yace:

“ Jamuna ,Akasa,mungama”.sai mutane gaba days suce ga tsumburbura ga magajin Dala.”

Sai ya koma saman Dutsen Dala jama’ar nan tana biye dashi tare da abin hadayarsu su sai a yayyaka su. Sai kuma shi barbushe yace:

“ Nine magajin Dala da kunki da kun so “. Su kuma sai suce “mai gida mun bika “

Sannan sai kowa yayi tsirara mazan su da matan su su kewaye ginin da tsumburbura take ciki, shi kuma barbushe sai ya tafi da manyan su kofar dakin tsumburbura suyi sujada. Shi kuma sai ya shiga wurin tsumburbura bazai fito ba sai da safe ,in ya fito sai ya basu labarin abinda zai auku a wannan shekarar kamar yadda ya jiyo daga bakin tsumburbura.

Masana tarihi na cewa Barbushe jika ne na kimanin 15 ga mutumin da ya fi shahara cikin wadanda suka fara zama a garin, kuma aka bai wa birnin sunansa wato Kano.

Bayan zamanin Barbushe da kimanin shekara 200 aka samu wasu mutane daga yankin Daura da suka ci Kano da yaki suka kafa sarauta a karkashin Bagauda a shekarar 999.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »