YAU TAKE RANAR HAUSA

0 729

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A yau ne 26 ga watan ogusta 2019 ake bikin ranar harshen Hausa ta duniya, harshen da ya zama na goma sha daya a duniya da aka fi amfani da shi.

Sai dai kuma kash masana na kukan cewar tasirin turawan mulkin mallaka na cigaba da kawowa Yaren cikas wajen harkar koyo da koyar da harshen.

Ranar Hausa

Yaudai shekara biyar kenan da wasu masana akan harshen hausa suka kirkiri wannan rana ta 26 ga watan ogusta ta zama ranar hausa ta duniya.

Inda duk wani gidan redio da talabijin da kuma shafukan sada zumunta ake tattauna batutuwa masu muhimmanci akan shi kansa YAREN HAUSA.

Don haka shafin Alummar Hausa shima yadan kawo nasa wasu batutuwan akan Yaren na Hausa kuma yansa ran cewa mabiya wannan shafi suma zasu kawo wata karin magana kokuma Wani muhimmin batu wanda ya kunshi Hausawa.

GASU KAMAR HAKA:

  • Aure nesa maganin diya mai yaji.
  • Mai akuya ya bi dare bare mai kura.
  • Kowa ya raina gajere to bai taka kunama ba.
  • Abin al’ajabi ango ya kwana da kunzugu.
  • Rokon allah maganin wayyo allah.
  • Ai ganin laushi baya hanani tankade.
  • Ya na iya da abin da wuta taci ta rage inji kishiyar konanniya.
  • Na ta6a ki da alheri, wai kishiya ta ta6a kishiya da bakin wuta.
  • Idan kana cin kasa kakiyayi ta shuri.

Mungode akafta!!

Wannan video na kasa wata daddar hausa ce daga bakin Bilkisu Tambuwal asha kallo lafiya.

Yauce Ranar Hausa, You anda Zamuji Wani Bayani Daga Bakin Bilkisu Tambuwal Asha Kalli Lafiya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »