TARIHIN INGAWA A JIHAR KATSINA

6 1,848


INGAWA TA DAMBO KUNU SAI YAADA

Garin ingawa yana Gabas da Birnin Katsina. Tsohon gari ne mai ganuwa wadda aka ce Habe suka gina ta tun kafin zuwan Fulani. 
Ainihin fulanin da suka zo daga baya, suka zauna a ingawa, su ne fulanin yarimawa.wasu masana Tarihi sunyi bayanin yanda fulanin suka zo garin ingawa, inda aka danganta asalinsu da zuri’ar Fulanin da ake kira da Ardo Kuru-Kuru. Sun yi kaura zuwa Barno, inda suka samu karbuwa, musamman gun wani basaraken masarautar Barno, Wanda ake kira Yarima.
Saboda shakuwar Fulanin Ardo da Yariman Barno. Sai suka samu lakabin yarimawa. A wajen karni na 17, wadannan Fulani na yarimawa da wasu kungiyoyin Fulani sun bar Barno saboda sabanin da suka samu tsakanin su da sarakunan Barno din. Wasu daga cikin kungiyoyin Fulanin sun yi kaura zuwa sandamu da Gamagira da ke Daura. Wasu kuma suka tsaya a Danbatta da ke Kano, wasu kuma suka tsaya a Yamel da ke Katsina. 
Kamar yanda masanin Tarihin nan Bala Usman ya ce, kungiyar Fulani da suka zo Katsina, suna karkashin wani Bafillatanin da ake kira inti,wayanda sarakunan Katsina na wancan lokacin suka karbesu, su ka bashi gurin zama, kuma aka bashi shi inti din sarautar Sarkin Fulanin Dambo, Wanda fadarsa ke ingawa ta yanzu. 
Wannan sarauta da aka ba inti ta Sarkin fulanin Dambo, ta sa inti yazama shugaban Fulani, ba na gabacin kasar ba kawai harma Dana wadansu wurare kamar su koda da shimya da kurfeji da Doddoji da Bawaji. Saboda wannan karamci da sarakunan Haben Katsina suka yiwa yarimawa yasa suka ba sarakunan goyon baya, Wanda yasa koda jihadi yazo baisa suka canza goyon bayan nasu ba ga sarakunan Haben ba. 
Wannan Dalilin ne ma yasa Dantunku yarika yakar yan’uwansa Fulani Wanda shima bayarime ne, a ingawa. 
Garin ingawa, wuri ne mai ni’ima da ruwan fadama da wurin yin kiwon Dabbobi. Wannan ni’imar da Allah yaba gurin ita ta janwo hankalin yarimawan da ke gurin. Baya ga haka, kuma ga karfen tama da ake a kasar ingawa din baki daya. Bugu da kari, ingawa ta kasance a kan hanyar da ta taso daga Maradi da Damagaram da Katsina, ta bi ta ingawa zuwa Rano. Saboda wannan ne ma yasa garin ya zama gurin kawo hari. Shima Yakudima ya taba kawo wa garin hari daga Damagaram. Amma saboda wannan ganuwa ta ingawa wadda za a iya kwatanta ta da ta Birnin Katsina, duk lokacin da maharan suka kawo hari, basu samun shiga garin ballantana aci garin da yaki. 
Kamar yanda muka fadi a baya, a kwai zumunci na yan uwanta tsakanin fulanin dake ingawa da wayanda suke a kandawa da kurfeji da na kazaure da na ‘Yandoma da sauransu. Kamar yanda muka fadi a baya koda jihadi yazo yarimawa basa juyama sarakunan Haben Katsina baya ba sun basu Goyon baya, amma daga bisani sunyi biyayya kuma an barsu akan sarautar su ta Sarkin fulanin Dambo. Majiyarmu ta nuna cewa, tun daga lokacin da aka Nada inti Sarkin fulanin Dambo ya zuwa yanzu anyi  Dambo kamar 40. 

Wasu daga cikin su ne,

  • Dambo kurukuru da 
  • Dambo jibo da 
  • Dambo Suleiman da 
  • Dambo Gere, 

wadanda ba a samu shekarun da suka yi sarauta ba. Sun hadar da

  • 1- Dambo Mazadu Dan Maza waje 
  • 2- Dambo Sa’idu 
  • 3- Dambo Muhammadu Bello 
  • 4- Dambo Tukur Murabus 
  • 5- Dambo Ibrahim 
  • 6- Dambo Abubakar 

( Amma shi wani masanin Tarihin Dankoussou cewa yayi sarakunan Dambo sune kamar haka

  • 1- Yarima inti 
  • 2- Sarkin Fulani Geeza 
  • 3- Sarkin Fulani jabir 
  • 4- Sarkin Fulani yalando 
  • 5- Sarkin Fulani kutuma 
  • 6- Sarkin Fulani Bagwari 
  • 7- Sarkin Fulani Marabu 
  • 8- Sarkin Fulani Danko 
  • 9- Sarkin Fulani Mazawaje mai Rijiya 
  • 10- Sarkin Fulani Yakubu Gaga
  • 11- Sarkin Fulani Malaladu 
  • 12- Sarkin Fulani Dambo 
  • 13- Sarkin Fulani Muhammadu Bello idi 
  • 14- Sarkin Fulani Muhamman Tukur 
  • 15- Sarkin Fulani Iro mai kaita. 

Wayanda muka samu kenan sunayen wayanda bamu saba mai karatu sai ka karisa mana ( INGAWA TA DAMBO KUNU SAI YADA)

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

  1. Aminu abubakar says

    Allah yakarawa annabi daraja amin daga aminu ingawa ma zaunin kaduna

    1. admin says

      Amin Thuma Amin Mal. Amin

  2. Mustapha sani says

    Allah kai mai garin ingawa albarka Mustapha sani mande dan mutan ingawa
    08061294304

  3. Sani dankawu rugar idi says

    Allah ya karama jahar katsina albarka
    Dama lanjeria baki daya amma ya

    Bakusa tarihi garin rugar idi. Ba

  4. Sani dankawu rugar idi says

    Allah ya karama jahar katsina daukaka
    Dama Nigeria daki daya amma ni dan
    Bindawa ne kauyen rugar idi ina alfahari
    Shi ya bakusa rugar idi

  5. alummarhausa says

    Muna kan binciken labarin amma idan kana da wani daga ciki zaka iya bamu . mungode

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »