TARIHIN SAMUWAR SANAOI A KASAR HAUSA

1 1,639

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 TARIHIN SAMUWAR SANA’O’IN GARGAJIYA NA HAUSAWA 

Tarihi ya nuna cewa, tun zamanin ‘ya’yan Annabi Adamu wato Kabila da Habila sana’ar ta  fara wanzuwa a doron kasa. Ta hanyar sarrafa itace a matsayin garma da ake noma da ita. Ashe ke nan, samuwar sana’a wani dadaden tarihi ne da ya fara wanzuwa tun farko halittar bil-Adama.
Tabbacin tarihin samuwar sana’o’in gargajiya na Hausawa abu ne mai wuya ga al’ummar Hausawa. Amma akwai hasashen dake cewa sana’a ta dan Adam akwai dalilan da suka samar da ita.
Tun kafin wannan nazarin akwai fahimtar cewa bukatoci daban-daban na dan Adam su ne suka haifar da samuwar sana’o’i daban-daban na dan Adam saboda samun saukin tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum.
Daga cikin bukatun dan Adam akwai “abinci” bukatar abinci, ita ce ta haifar da sana’ar “noma”. Domin babu wata rayuwa da ke inganta, ba tare da abinci ba. Saboda haka, idan za a samar da abinci, sai an nemi kayan aiki yin noma. Wannan hanya ce ta samar da kayan aikin noma ta haifar da sana’ar “kira”.
Ire-iren wadannan bukatu ne suka haifar da samuwar wasu daga cikin kananan da manyan sana’o’in gargajiya na Hausawa.
Alal misali, bukatar sutura ce ta haifar da sana’ar “Saka”. haka ma bukatar ingantaccen muhali, ya haifar da sana’ar “gini”. Haka dai abin ya cigaba da wanzuwa har  zuwa lokacin da tunanin Hausawa ya fadada, bukatun su suka karu. Saboda haka sai sana’o’i suka karu har suka samar da cikakkun abubuwan gudanar da rayuwar al’ummar Hausawa ta yau da kullum.
Akwai hasashe cewa ta haka ne sana’o’in gargajiya suka bunkasa kuma kowace zuriya ta kama sana’ar da ta fi dacewa da ita.
Har wa yau hasashe ya nuna I’m  sana’o’in gargajiya sun taimaka wajen kafuwa da bunkasar unguwanni da kauyukka da biranen a kasar Hausa. Don fahimtar haka, ana iya kallon wasu unguwanni a manyan garuruwan kasar Hausa. Misali.
 • Unguwar makerar Assada Sakkwato 
 • Majema unguwar Rogo Sakkwato
 • Marina, ‘yan marina, Sakkwato
 • Unguwar ‘yan gurasa, Kano
 • Marnan gangu, Sakkwato,
 • Madaka Sakkwato
 • Madun}a, Sakkwato, Kano

Haka kuma akwai

 • Unguwar ‘Yan Awaki- Kano
 • Unguwar Sakkarawa- Sanyinna
 • Unguwar Wanzamai- Sanyinna
 • Unguwar ‘yan kifi- Kano
 • Kasuwar ‘yan Gwari- Kano
 • Unguwar ‘yan Taba-Katsina

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 1. Ahmad muhammad b inna says

  Muna godiya, kuma buna bukartar musa ya ta samo asali a hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »