Wanann shine cigaban tarihin masarautar jihar Gombe.
YADDA GOMBE TA SAMO ASALIN SUNAN TA
Daga baya Buba Yero da dan uwansa sun hada hannu da kuma karfi da karfe wajen ci gaba da Jihadi, inda suka ci kabilar Fali da yaki, bayan an yi gwajin kwanji da kuma dauki-ba-dadi a garin Burmi (wanda ake kiran yakin da suna Yakin Burmi na 1).
Sun shiga garin Kororofa babban birnin masarautar Jukun, inda a nan Buba Yero ya dora lura da wajen a hannun Hamma ruwa, sakamakon zargi da Buba Yero ya yi na cewa za su iya daukar fansa. Daga nan sai Buba Yero ya zauna a wani waje da ake kira Gumbol Ribadu, wanda yanzu yake karkashin masarautar Nafada, a cikin shekarar 1814. Ya zauna har tsawon shekara 7.
Daga nan ya koma yamma da Dukku, aka rada wa garin suna Gombe-Abba, wanda har yanzu ana kiran garin da haka. Daga nan Buba Yero ya aiki Magajin Garin Gombe-Abba, da ya nemo masa wajen da zai yi dadin zama.
Bayan ya fita nema ne ya samo wani waje kusa da wani tsauni da yake yamma da Dukku, nisan wajen daga Dukku Mil 19 ne.
A nan Buba Yero ya gina gida kusa da wata bishiyar kuka da ‘yan kabilar Bolewa masu bauta mata ke kiran ta da Gombe-Memositi. Wasu daga cikin Bolewa sun sauko daga tsaunikansu, suka kuma zauna tare da Fulani su ( Buba Yero), daga nan kuma aka fara kiran garin da Guru-Gombe-Memositi.
Ana cikin haka kuma sai auratayya ta shiga tsakanin Bolewa da kuma Fulani. Da tafiya ta yi tafiya, sai suka fara kiran garin da suna Gombe. Bayan an gina garin Gombe ne, sai kuma ya ci gaba da Jihadinsa, inda da shi da dakarunsa, suka karkata gami da sa gabansu arewa.
A karshe suka hadu da dakarun Shehu Dan Fodiyo, sannan suka tunkari birnin Ngazargamu (babban birnin masarautar Barno), wanda sun yi hakan ne bayan sun yi galaba a garin Darazo da kuma Logo.
Bayan wannan lokacin ne sai Buba Yero ya samu sabani da dan uwansa Hamma ruwa (sarkin Muri 1883), wanda hakan ne ya zama ummul’aba’isin da al’ummar Jalingo suka mika kukansu ga Shehu kan a ba su ‘yancin kansu daga kasar Gombe. Shehu ya karbi kukansu, ya kuma share musu hawaye, inda ya ce da su cikin ‘Kirdi’ (Fulfulde), cewa ya ba su ‘yanci, amma har yanzu sun kasa karbar tutar Jihadi, wannan dalilin ne ya sa har yanzu ake kiran fulanin Jalingo da sunan ‘Fulani-Kiri’.
Buba Yero ya mutu a shekarar 1841 Buba Yero bai yi mulki ba, ya dai kafa masarautar Gombe ne. Bayan ya rasu ne, aka fara mulkin sarauta, wanda ake kiran sarki da ‘Modibbo Gombe’.
Kamar yadda na yi bayani a baya cewa, Buba Yero ya auri Zulai ‘yar gidan sarkin Katsina, wanda a kan hanyar sa ta dawowa ne, aka haifa masa Sulaimanu a wani waje da ake kira Shani karkashin ikon Biu, wani gari a masarautar Barno.
Sulaimanu ne ya zama sarkin Gombe na farko. Bayan Buba Yero ya bar garin Shani ya koma Gulani ne, matarsa ta biyu Hauwa (‘Yar sarkin Daura), ta haifa masa da namiji, wanda aka sanyawa suna Muhammadu Kwairanga, wanda kuma shi ne ya zama sarkin Gombe na biyu. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake kiran masarautar Gombe da ‘Shanima Gulanima Fulbe Janafulu’.
YAKIN BURMI NA BIYU (2/ ga watan Jimada Akir,1320A H daidai da 27-Juli, 1903) Wannan yakin yana da matukar mahimmanci a tarihin kafuwar garin Gombe, kasancewar bayan yakin ne garin Gombe ya hau wata turba har zuwa yau. Sai dai kafin nan bari na dan yi baya da mai karatu.
A zamanin sarkin Gombe na shida wato Umaru (1899-1922), an samu hauhawar kaurar mutane zuwa Gombe, ciki har da korarru da tubabbun sarakunan Arewa, wadanda Nasara masu jajayen kunnuwa suka hambarar. Wadanda suka hada da: sarkin Misau Ahmadu na biyu (1900-1902) da sarkin Keffi Magaji Dan Musa da sarkin Malle Basiru da sarkin Bida da dai sauran masu fada a ji da talakawan da suka sha alwashin ba za su zauna karkashin mulkin Nasara ba.
Wadannan mutane sun yi kaura daga garuruwa irin su Kano da Gombe da Bauci da Misau da Bida da sauransu. Sun ce ba za su zauna karkashin gwamnatin Sa Fredrick Lugard ba. Bayan sojojin Nasara a qarqashin Lugard sun ci karfin Kano da Hadejiya ne, sai suka tattaro hankalinsu garin Gombe, kasancewar sun samu labarin kusan dukkan tubabbu da korarrun sarakuna sun hadu a garin Burmi.
Kamar yadda ruwa ba ya tsami a banza haka Nasara ya san tun da wadannan sarakuna suka taru a waje daya, to sun san ko badade, ko ba jima komai zai iya faruwa. Bugu da kari ga Sultan Attahiru ma na garin Burmi. Kuma dama Sultan Attahiru ya samu labarin Faransawa suna jiran sa a tafkin Chadi, kasancewar ita ce hanyar da yake bi, idan zai je aikin Hajji ko Ummara ke nan.
Wani zafi-a-kan-zafi kuma shi ne, ga Fadel (dan gidan Rabeh) da mutanensa suna jiran sa a kudancin Burmi. Kasancewar garin Burmi ne da yawancin wadanda suka yi Jihadi suke, sai suka yi ittifakin ko da sama da kasa za su hadu, to sun shirya kare Burmi.
Wannan shi ne dalilin da Sultan Attahiru ya shirya wata tawaga ta malamai da sojojin yaki da aka sanya wa suna ‘Ferol’.
A ranar 27 ga watan Yulin 1903 Manjo F.C Marsh ya iso garin Burmi, sannan ya yi sansaninsa a kusa da shiga garin. Bayan ya yi kwanaki uku ne, sai kazamn yaki ya barke a wajen, inda aka yi ta karon-battar-karfe, fito- na-fito da kuma dauki-ba- dadi.
Jinin mayaka sun zuba Inda a karshe sojojin Nasarawa suka yi galaba. Sai dai kuma Sultan Attahiru da kuma Manjo F. C Marsh duka sun rasa rayukansu a yakin da aka yi a garin Burmi.
Wanda har a yanzu kuma kaburburansu suna garin na Burmi.
Karanta