Hausapeoples
Tarihin garin Kura ta jihar kanon Nigeria 🇳🇬 mai sauraro asha karatu lafiya.
GARIN KURA
Garin kura ya samo asali ne a kan shahararren Kogin da ake kira Rafin Kura a kudancin garin, wanda ake yin amfani dashi don aikin noma da kuma shayar da dabbobi, Æ™arni da suka wuce. Babu shakka yana da matukar wuya a samu ainihin shekara ko zamanin da mutanen Kura suka zauna a wannan Æ™asa mai ban sha’awa.
Amma abin da aka sani shi ne cewa, Kura ta zo ne a cikin karni 18 bayan an gano ta a matsayin hanya da kuma sansani na Larabawa da Abzinawa da yan kasuwa.
A wannan lokacin, ana samun mutane ne kawai a wuraren kamar Alkalawa, Limamai, Yalwa, Rimin Daddo, Unguwar Gandu, Unguwrar Bugu da dai sauransu.
A wannan lokacin kasuwancinsu na gida shine ya hadar da aikin Gona, Kasuwanci, Saƙa, Rini, da kuma farauta. Sannan suna samar da Rawani (Rawani Dan Kura) a gida.
Rawani dai Sarakunan gargajiya sun yin amfani da Rawani, dattawan maza, masu arziki da kuma malaman Islama.
An san mutanen Kura ta hanyar Æ™arfin zuciya da kuma sadaukar da kai ga wadannan al’adu nasu na gida. Fiye da kashi 99% na duka yawan jama’ar dake Kura Musulmai ne kuma mafiya yawa Hausawa ne, sai Fulani, da kuma Kanuri.
Garin ko wurin nada sararin Æ™asa mai ban sha’awa da kuma kyau wajen yin shuke-shuke masu kyau.
Saboda haka, Kura na daya daga cikin kananan hukumomi 44 a yankunan Jihar Kano da ke a kudancin jiha, garin nakusa da Babban titin Hanyar Zaria-Kano wadda yake da nisan kimanin muraba’i 35Km daga babban birnin jihar. Ya kasance a 11 46 ’17 “N zuwa 8 25’49 “E.
Sannan jihar nada girman kasa da yakai kimanin muraba’i 206km (80 sq mi) na Æ™asa mai cinye tare da yawan Jma’ar da yakai kimanin 144,601 a kidayar shekara ta 2006. Har ila yau, yana hannun Riga KO iyaka tare da Garun Malam a yamma kuma , yankin Madobi daga Arewa, Yankin Dawakin Kudu daga Gabas Bunkure kudu.
Haka zalika yanzu haka mutanan Kura kashi 80% cikin Dari manoma ne inda suke samar da kayan gona Rani da Damuna
Wasu daga cikin albarkatu Gona daKur ke samarwa a yankin su ne Shinkafa, Alkama, Masara, Gero, Masara, Tumatir, Albasa, Kokwamba, Kabeji, da dai sauransu.
Karamar Hukumar Kura nada unguwani kamar haka:
1. DALILI,
2. DAN HASSAN,
3. DUKAWA,
4. GUNDUTSE,
5. RIGAR DUKA,
6. KARFI
7. KOSAWA,
8. KURINSUMAU,
9. SARKIN KURA,
10. TANAWA