TARIHIN MASARAUTAR GUMEL TA JIHAR JIGAWA

0 2,117
Wannan shine tarihin masarautar Gumel ta jihar jigawa
An kafa masarautar Gumel ne a shekara ta 1750, Kuma wani mutum ne mai suna dan-juma ya samar da ita wanda yake a jihar Kano dashi da mutanansa daga kabilar Mangawa. 
Ba daɗewa da rasuwar sa ba a shekara ta 1754, sai ya zama jihar ta zama mai biyan haraji na mulkin Bornu. 
Masarautar Gumel sun tsira daga hare-haren Fulani na jihadin Usman Dan Fodio a farkon karni na 19th kuma ba ta zama wani ɓangare na Fulanin daular Sokoto ba. 
Yankin yanzu na Gumel yasamo asali ne sakamakon wata hijira da akayi a shekara ta 1845 daga garin Tumbi, wanda ke cikin Nijar. 
Masarautar Gumel takasance tana yawan samun hare hare na yaQi akai akai daga yankunan da suke kusanci da ita kamar Hadejia, Danzomo, Kano da kuma Zinder tun a shekara ta 1828.
YaQi tsakanin Gumel da Hadejia yaci gaba da faruwa har saida sarkin Gumel Abdullahi ya mutu a shekara ta 1872.
Kafin Ahmadu ya amince da mulkin da kuma dokokin Birtaniya a shekara ta 1903.
A shekara ta 1976 Gumel tazama wani bangare na jihar Kano, 
Sannan a shekara ta 1991 Gumel ta zama daya daga cikin ɓangare na Jihar Jigawa kusa da Danzomo, Gagarawa, Sule Tankarkar, da kuma Maigatari.
Haka zalika Karamar hukumar Gumel nada unguwani guda 11 sune kamar haka:
1.Baikarya
2.Danama
3.Dantanoma
4.Galagamma
5.Garin Alhaji Barka
6.Garin Gambo
7.Gusau
8.Hammado
9.Kofar Arewa
1 0.Kofar Yamma
11.Zango
Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa
Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »