TARIHIN SIYASAR NIGERIA KASHI NA DAYA (1)

3 3,568

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kashi na ɗaya.

Tarihin siyasar Nigeria kusan yana tafiya kafaɗa da kafaɗa ne da tarihin samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, da kuma wasu abubuwa da suka wakana kafin wanzuwar hakan.
  Da fari dai, gwamnatin ingila ta ayyana ɗaukacin yankunan da ayau ake kira Nigeria bisa karkashin ikonta a ranar 1 ga watan janairun shekara ta 1901, har kuma ta aike da sojoji domin karɓe ikon yankunan baki ɗaya.
   Yankunan Kano da Sokoto ne kusan na karshe da suka faɗa hannun turawan mulki a wajajen shekara ta 1903 zuwa 1904. Tun daga nan kuma Sir Lord Luggard ya zamo shine ɗaukacin shugaɓan tarayyar Nigeria.
   A wancan zamani, babu maganar kafa jamiyyar siyasa, ko kungiyoyi. Maganar biyayyar dokokin turawa kurum akeyi ta hannun sarakuna. Kuma akwai doka da hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi shelar neman ‘yanci daga turawan mulki.
 Mutanen arewa nada matukar jahilci a fannin ilimin boko duba da kalilan daga cikinsu ne suka sanya yaransu a makarantun zamani. Don haka, kururuwar kafa jam’iyyun siysa da neman ‘yanci bata soma kaɗawa ba da wuri-wuri a yankin.
    Sir Lord Luggard, ya gudanar da mulkinsa ba tare da kulawa da ra’ayin ‘yan kasa ba, sai dai bisa umarnin kasar sa ingila. Amma duk da haka, yana da majalisa ta jeka na yika, mai ɗauke da wakilai 26 waɗanda suka kunshi wasu daga sarakunan gargajiya a kudanci, waɗanda kuma akasari karɓar umarni ne kurum ne aikinsu, kuma ba zaɓensu akayi ba a siyasance.
    Sai a zamanin mulkin Sir Hugh Clifford ne aka soma kafa ɓurɓushin dimokaraɗiyya a Nigeria. A wuraren shekara ta 1920 ya bijiro da kundin tsarin mulki sassauka, wanda aka lakabawa sunansa, wanda kuma ya sahalewa ‘yan kudancin kasar nan damar zaɓen wakilai huɗu daga cikin ‘yan majalisar kasa ta jeka na yika.
   Koda yake, sauyin da ya kawo daga gwamnatin Luggard shine kafa majalisu guda biyu a kasa. Daya itace majalisar zartaswa, wadda turawa ne zallah a cikin ta. Sai kuma majalisar kasa mai ɗauke da wakilai 46.
Masu Alaka
1 of 5
   Acikin waɗannan wakilai 46, kusan kafataninsu turawa ne da gwamnati ta naɗa suke kula da kasuwancin Lagos, kano, Calabar da Phortharcort, sai kuma guda 6 ‘yan kasa da gwamnati ta naɗa a matsayin wakilai.
 Acikinsu akwai mutum ɗaya yana wakiltar ‘yan kasuwar Afirka, ɗaya yaana wakiltar gundumar lagos, ɗaya Egba, ɗaya Ibo ɗaya kuma Oyo. Babu ko ɗaya daga arewa.
   Wakilai huɗu kuwa akace an sahale a shiga zaɓe domin a zaɓosu. A lokacin an bada wakilai uku a lagos, wakili ɗaya kuma daga Calabar.
Saboda haka, a wannan shekarar ta 1923 sai Herbert Macaulay yafara kafa jamiyyar siyasa a Nigeria mai suna ‘Nigerian National Democratic Party (NNDP)’ domin shiga zaɓen cike gurɓi na majalisar kasa da kuma samar da shugabancin birnin Lagos.
   Herbert Macaulay daman sanan-nen ɗan gwagwarmaya ne kuma mai ilimi tun a wancan lokaci. Tunda kuwa ya karanci fasahar kasa da safayo a Ingila tun gabannin shekarar 1900. Kuma ya shiga kungiyar dake rajin kawar da cinikin bayi a yankin Afirka.
   Sannan tun kafin wannan lokacin, yana takun saka da turawan mulkin mallaka, musamman yadda yake fafutikar kwatowa ‘yan kasa yancin kai.
   A shekarar 1908 Herbert Macaulay ya bankaɗo al-mundahanar da wasu jami’an mulki turawa sukayi wajen gina titin dogo, wanda kowa ya sani da arzikin Nigeria ake yinsa.
   Sannan a shekarar 1919, Herbert Macauley ne yakai kara izuwa majalisar Ingila yana nemawa wani shugaban yankinsu da aka kwace masa fili. Kuma ya samu nasara, inda majalisar ta zartar da hukuncin a biya waccan shugaba diyyar daya nema.
  Anyi zaɓe na farko a ranar 20 ga watan satumbar shekara ta 1923. Ance a lokacin, waɗanda sukayi rijistar kaɗa zaɓe a cikin mutum dubu 99 mazauna lagos mutum dubu 4 ne kachal. Saboda haka an shiga zaɓe cikin lumana da kwanciyar hankali babu tasgaro, saboda duk ɗan kasa cike yake da tsoron idan ya aikata laifi turawa zasu hukuntashi.
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Suleiman Musa says

    Salam

    1. admin says

      waalaikumussalam

  2. […] KARANTA TARIHIN NIGERIA 🇳🇬 KASHI NA DAYA 1 […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »