A ranar Lahadi 17 ga watan Afirilu ya yi daidai da Lahadi 17 ga watan Afrilu 2016, shekaru 33 kenan da rasuwar Malam Aminu Kano, wanda ‘yan uwansa ‘yan siyasa suke yi masa lakabi da kirari da suna Malam Aminu dan kasa na gari, saboda kishinsa ga al’ummar Arewa da kuma imani da ya yi akan tsari irin na adawa.
Shekaru 30 Malam Aminu ya yi yana jam’iyyar adawa domin fafutukar ya
samawa talaka ‘yanci da kubuta daga kangi na danniya da zalunci da ake
masu a lokacin mulkin mallaka na Turawa da kuma bayan an samu ‘yanci
kai daga Turawan mulkin mallaka.
Masana tarihi akan rayuwar Malam Aminu Kano sun ce Malam Aminu shi ya fara koyawa talaka yadda zai iya yin tirjiya idan an zalunce shi, kana a karon farko talaka ya fara koyon cewa (a’a) a ba ni hakkina, a lokacin talakawa suna noma a gandun Sarki kyauta babu kudi.
Wani abokin Malam Aminu kuma al-majirinsa a siyasa, wato mallam Lawan Danbazau a wani dan karamin littafi da ya taba rubutawa akan tarihin rayuwar Malam Aminu Kano,
Littafin wanda ya sanyawa suna ‘DAN AREWA NA AINIHI MALLAM AMINU
KANO’, a cikin littafin Malam Lawan Danbazau ya bayyana cewa abubuwa
guda 5 mallam Aminu ya kuduri aniya zai yi na daga fuskar sana’ar zaman
duniya amma daga karshe babu wanda ya samu, sai a cikin wanda ba a zata
ba ya rayu har ya mutu a cikin ya tabbata wato shugabanci kenan ko kuma
siyasa.
Da farko ya so ya zama Lauya amma saboda sanin halinsa sai maganar ta girgiza (Resdan) na Kano na waccan lokacin domin kowa ya san halin Malam Aminu Kano na yaki da akidun turawa na danniyya da zalunci tun yana dan makaranta a middle, dan haka in ya samu dama ya zama Lauya, to zai futuni Turawa akan bakin mulkin su na mulkin mallaka, saboda haka sai aka dakile maganar ba ta je koina ba na biyu sai ya ce yana so ya zama likita, nan ma aka ce babu isassun yaran da za’a hada su su je izuwa Lagos makaranatar koyan aikin Likita
dake Yaba a Logos.
Na uku sai ya ce yana so ya yi aikin Dan sanda nan ma sai aka ce masa tsahon sa bai kai ba da inci 6. Na hudu, sai ya ce to yana so ya zama malamin Asibiti nan ma aka ce a’a sai da ya yi aikin koyarwa a makaranta, shi kuma sam bai cika son koyarwa ba. Dan haka idan an duba to za aga cewa a cikin duk aiyukan nan biyar da aka lissafo, to babu wanda Malam Aminu bai yi su ba, domin a cikin zuciyarsa duk ya yi su ko da bai samu aikatawa da hannunsa ko kuma da bakinsa, ya aikata wanda da a ce so samu ne ace hannun sa ne suka aikata.
A cikin shekaru sittin da uku da Malam Aminu ya yi a rayuwar sa, to fiye da
shekaru talatin da ya dauka yana hidima a siyasa wanda
makusantan sa wadanda suka yi tarrayya da shi a siyasa su ka ce a kullum
tunanin Malam idan garin Allah ya waye ba ya wuce abu daya, wato yadda
za’a kyautatawa zaman jama’a, kana talakan kasa ya san masu
shugabancin sa sun san da zaman sa da abin da ke damunsa.
Da yawa mutane sun dauka cewa gaba ce kulalliya tsakanin Malam Aminu da Firimiyan jihar Arewa, Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello, to amma sam ba haka abin yake ba, domin tun bayan mutuwar Sardauna an jiyo Malam Aminu a laccocin sa daban-daban yana yabon Sardauna a wajen gaskiyar sa da rikon amanar sa da kuma shugabanci nagari.
Malam Aminu shine jagoran Jam’iyar NEPU duk da yake dai ba ya daya daga
cikin mutane takwas din da suka kafa NEPU a 1948, amma tasirinsa a cikin
Related Posts
jam’iyar ya sa talakawa suka dinga kwarara izuwa cikinta domin zama
memba, wanda a haka ya sa jam’iyyar ta yi karfi da farin jini a cikin
talakawa domin manufofin Malam Aminu shine yaki da akidun Turawan
mulkin mallaka masu ci da ceto musammanma yadda talaka yake biyan haraji
da jangali daidai da attajirai, har ta yi karfin da a waccan lokacin Turawan
mulkin mallaka suka fara gallazawa duk dan jam’iyar NEPU a dalilin cewa
wai talaka ya fara sanin hakkin sa da yin fito na fito da mulkin zalunci.
Za mu iya tunwa da Malam saboda sadaukauwar da ya yi domin talaka ya samu ya futa daga duhun jahilci da danniya. Duk wannan gwagwarmayar da Malam Aminu ya yi ya faro ta ne tun yana dalibi a sakandire. A lokacin da yake aikin koyarwa Turawa ‘yan mulkin mallaka sun yi ta ko karin su ga sun rufe bakin Malam Aninu akan yadda yake fallasa almubazzaranci da ake da kudaden haraji, saboda da haka sai aka tura Malam Aminu izuwa kasar Ingila domin ya yi kwas na shekara guda, bayan ya kammala kwasdin ya dawo gida mai makon ya yi shiru sai ya ci gaba da caccakar Turawa domin a lokacin an hana mahaifinsa, Alkali Yusufa ya zama Alkalin Alakalai na jihar Kano, saboda dalilin dan sa Aminu yana adawa da tsarin mulkin Turawa.
A karshe dai Malam Aminu ya rubuta wani dan karamin littafi mai kunshe da
raddi akan bakin mulkin Turawa, Liitafin da ya sanya wa suna ‘Kano Under
Hammer’ duk da haka aka kara yi masa tayin samun malamin jami’a mai
koyar da harshen Hausa a jami’ar Osfod dake Ingila.
Malam Aminu ya bar aikin koyarwa ya kuma tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan domin ita ce hanya kadai da zai bi ya kwatowa talaka ‘yancin sa ba tare da ya fuskanci barazana daga Turawan mulkin mallaka ba. A takardar barin aikin sa ya rubuta kamar haka “na hango wani haske a can nesa tsakanin sama da kasa dan haka zan yi kokari na riske shi ko da a ce ni kadai ne ko da wani”.
A shekarar 1920 aka haifi mallam Aminu Kano a birnin Kano, a Unguwar
Gwamaja. Ya fito daga zuri’ar Fulani Gyanawa, kana mahaifin sa malami ne
kuma alkali.
Ya halarci makarantar Elemantery ta Shahuci daga nan ya wuce kwalejin tarayya ta Katsina wacce a yanzu ta koma Barewa Kwaleji, ya kammala a 1937, daga nan aka tura shi koyarwa a Bauchi Training collage, da ya dauki lokaci a Bauchi, sai aka sauya masa gurin koyarwa izuwa makarantar sakandire da ke Maru a tsohuwar jihar Sokoto. A 1948 Malam Aminu shine ya fara kafa kungiyar kula da muradun malamai ta Arewa northern Teachers Association.
Malam Aminu ya fara tsayawa takarar zabe na farko a jam’iyar NEPU a
1954 ya fadi zabe a kokarinsa na zama dan majalisar tarayya, Danmasainin
Kano, Maitama Yusuf na jam’iyar NPC shi ya kada shi.
A 1956 ya kuma kara shan kaye a zaben da ya shiga na majalisar dokokin
jihar Arewa, sai a 1959 ya samu ya zama dan majalisar tarayya da gaggarun rinjaye na
kri’u, a can zauren majalisa dake Lagos aka nada Malam Aminu mataimakin
mai tsawatarwa na majalisa bayan jam’iyar NEPU ta yi kawance
da jam’iyar NCNC ta Azikuwe.
A lokacin da sojoji suka karbi mulki, Malam Aminu ya yi ministan Lafiya a gwamnatin Yakubu Gawan tsakanin 1967~1974. A jamhoriya ta biyu a 1979 Malam Aminu ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyarsa ta PRP, amma ya sha kaye a hanun Alh Shehu Shagari na NPN.
Malam Aminu ya rasu ranar Lahadi 17 ga watan April 1983, ya rasu ya bar matar sa daya, A’ishatu da ‘yar sa daya, Maryam. Haka zalika gida daya kawai ya bari da gona daya.
Daga Ado Musa