Tarihin Kafuwar Jamiar Sojojin Najeriya (Nigerian Defence Academy NDA)

1 636

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jamiar Sojojin Najeriya wadda akafi sani da (Nigerian Defence Academy (NDA)) dake jihar Kaduna, a Nijeriya itace jami’ar dake samar da horo na sojoji masu tsaron kasa wace ta zama ɗaya tilo mallakin sojin Nijeriya.

Ana shafe shekara biyar a makarantar, shekara huɗu a makarantar ana karatun ilimi a fanni daban daban kamar su ilimin Na’ura mai ƙwaƙwalwa, ilimin Yaren Faransanci, ilimin Tsaro, ilimin Kimiyyar Tsaro da Kwarewa, ilimin Lissafi, ilimin Fasahar Ƙere ƙere, ilimin Tattalin Arziki, ilimin Tarihi da Nazarin Yaƙi, ilimin Kimiyyar Siyasa da Dangantaka ta Duniya, ilimin Tsaro da Nazarin Tsaro, ilimin Larabci, ilimin Ƙididdiga, ilimin Kimiyyar Gudanarwa dadai sauransu.

Shekara dayan karshe kuma bayar da horon soja. Taken jami’ar itace “Aminci da Jaruntaka”, an Samar da makarantar ne a shekara ta alib 1964.

An samar da jami’ar ne tun a watan Fabrairun shekarar alif 1964 a matsayin sake gyaran tsohuwar makarantar sojin Kasar Biritaniya wato Royal Military Forces Training College (RMFTC), inda aka canja sunan zuwa makarantar horon soja (Nigerian Military Training College (NMTC)) a ranar samun yancin kai.

Jami’ar na koyar da Sojojin Ƙasa, Sojojin Ruwa, da kuma Sojojin Sama.

A karon farko jami’ar ta karantar da horar da mutane 62, kuma yawancin wadanda ke horarwanr sojojin kasar indiya ne, komandanta mai suna Brigadier M.R. Virma daga shekarar alif 1964 zuwa alif 1969 mutumin Indiya ne.

Makarantar ta zama ta yan Najeriya ne a shekarar alif ta 1978, sannan a shekara ta alif 1981 ta fara koyar da sojojin daga ko’ina a duniya.

A kuma shekara ta alif 1985 ne jami’ar ta fara horar da sojoji da suke bakin aiki da kuma bayar da shaidar digiri na biyu da na uku ga sojoji da kuma waɗanda ba sojoji ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] post Tarihin Kafuwar Jamiar Sojojin Najeriya (Nigerian Defence Academy NDA) appeared first on Alummar […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »