TARIHIN SIYASAR NIGERIA KASHI NA UKU (3)

0 4,356

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

KASHI NA UKU

Turawan mulkin mallaka sun rinka shugabantar talakawan yankin Arewa karkashin sarakunan mulki na gargajiya abinda ake kira a turance ‘Indirect Rule’.
   A lokacin, an ragewa sarakuna karfin iko ta hanyar samar da wani tsari mai suna ‘Native Authority’ (NA) wanda ya kunshi Sarki mai kula da talakawa da karɓar haraji, sai Alkali mai kula da shari’o’i, da kuma Ma’aji mai kula da baitil malin abinda sarakuna suka tatyara. Don kowanne sarki zai fita likaci-zuwa-lokaci tattaro haraji da jangali wanda turawa suka kakabawa ga ‘yan kasa.
   Sannan kowanne magidanci tilas ya tanaji kuɗin da zai biya a matsayin haraji akan kansa da wurin kasuwancinsa. Sannan akan ‘ya’yansa maza ma akwai haraji da ake biya.
   Kasancewar yankin Arewa bai tumbatsa da masu ilimin zamani ba, wutar neman ‘yanci da kawar da talakawa daga wannan kunci bata soma ruruwa da wurwuri ba a yankin, abinda kurum akafi sani shine an haramta cinikayyar bayi, to amma biyayyar da talakawa ke yiwa sarakai bata canza ba, duk kuma wanda yayi yinkurin tada kayar baya ko bore yanzun nan zai haɗu da fushin ‘yandoka.
      Mutumin da kusan za’a iya cewa shine ya fara kawo tunanin samar da kungiyar kwato yanci a yankin Arewa shine Mallam Sa’adu Zungur bayan yaje Lagos yin karatu yaga yadda su Dr Nnamdi Azikwe da Herbert Macaulay dasu Awolowo ke fafuti ga yankunansu, sai ya assassa kafa wata kungiyar malamai mai suna ‘Zaria Literary Society’ a shekarar 1939 sa’ar da aka tura shi aikin koyarwa a makarantar kula da lafiyar muhalli ta zaria. Daga baya sunan kungiyar ya sauya izuwa Zaria Improvement Union a shekarar 1941.
 Sa’adu Zungur ya shiga faɗakar da masu ilimin boko ‘yan uwansa na zamanin cewar zaluncin da turawan mulkin mallaka sukeyi a kasa yayi yawa, domin ba haka akeyi a kasarsu ba. Sannan yace akwai bukatar kowanne majalisar Sarki ta N.A akwai zaɓaɓɓun wakilai masu bada shawara kamar yadda akeyi a Ingila zakaga akwai majalisu da suka kunshi wakilcin kungiyoyi da talakawa karkashin masarauta, waɗanda kuma suke da faɗa aji a wasu lamurori.
    A shekarar 1943 kuma sai wani ɗan gwagwarmaya mai rajin kwatar ‘yanci shima ya kafa kungiyar nemarwa mutanen arewa mafita daga kunchin da suke ciki mai suna ‘Northern Elements Progressive Association’ NEPA bayan ya samu ganawa da Dr Nnamdi Azikwe shugaban NCNC. Matashin ɗan kabilar Ebira ne mazaunin kano, sunan sa Habib Raji Abdullahi.
   A bauchi kuma, sai Mallam Sa’adu zungur da wasu malaman makaranta dake koyarwa a kwalejin Horarwa ta Bauchi irinsu Mallam Aminu kano da Abubakar Tafawa Balewa suka sake kafa wata kungiyar mai suna ‘Bauchi General Improvement Union’, daga baya suka tashi wata mai suna ‘Bauchi Discussion circle’.
    Ana haka sai jahohi suka rinka kafa kungiyoyinsu bisa ganin yadda ‘yan boko ‘yanuwansu ke kafa kungiyoyi don samar da cigaban jihar su. Ilimi da wayewar kai na zagayawa kenan sannu a hankali.
  A kan haka kungiyar Samarin Kano ta kafu, wadda Su Abdulkadir Adamu ɗan Jaji suka kafa, sannan Kungiyar samarin Sokoto  ta kafu wadda su Shehu Shagari, Ibrahim Gusau, Ahmadu Bello da Sani Dingyaɗi suka shiga a Shekarar 1947.
   Waɗannan kungiyoyi sun kira zama domin samar da haɗin kai a zaria a tsakanin shekarar 1947 zuwa 1948 amma zaman ya tashi babu nasara bisa zargin akwai ‘yan leken asirin sarakuna acikin mahalarta taron.
   A wannan lokaci kuwa, zamanin mulkin Shugaban kasa Sir. Arthur Richard ne, wanda yayi sabon kundin tsarin mulki har ya sahalewa majalisar yankuna harda yankin Arewa damar zaɓen wakilai, to amma gwamnonin turawa na arewa da sarakuna basu bada damar kafa jamiyyar siyasa ba. Don haka zaɓen da akayi na shekarar 1946 kusan indifenda akayi shi.
  A wannan zaɓen na 1946, aka zaɓi Alh. Muhammadu Ribaɗo ɗan majalisa daga Borno, aka kuma zaɓi Abubakar Tafawa Balewa ɗan majalisa daga Bauchi duk a zauren majalisar Arewa.
DAGA Bashir Tukur Gorzo

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »