TARHIN SIYASAR NIGERIA KASHI NA BIYU (2)

0 11,515

KASHI NA BIYU (2)

Bayan an kammala zaɓe, sai aka ayyana wakilai masu suna: Crispin Adeniyi Jones, Adeyemu Alakija da Egerton Shyngla na Jamiyyar NNDP ta Herbert Macaulay a matsayin waɗanda suka cinye zaɓe, don haka sun samu rinjaye akan ‘yan takarar da suka fafata dasu zaɓe daga Jam’iyyar ‘Peoples Union’ wadda  John K. Rindle da Orisadipe Obasa suka kafa. Sai kuma wakili ɗaya wanda yaci zaɓe ba tare da jamiyya ba daga Calabar.
   Ana haka sai Herbert Macaulay ya kafa kamfanin jaridar ‘Nigerian Daily’ da yake wayar dakan al’umma bisa kuncin da suke ciki na mulkin mallaka. Kuma jamiyyarsa ta samu tagomashin cinye zaɓuɓɓukan da aka gudanar a shekarar 1928, da kuma na shekarar 1933.
    Amma bayan shekaru biyar da kakar zaɓe ta kewayo, za’a sake shiga zaɓe a shekarar 1938, sai ya zamana wata jam’iyar yarabawa mai suna ‘Lagos Youth Movement’ wadda Farfesa Eyo Ita ya kafa ce ta lashe kafatanin zaɓen, ta ture Herbert Macaulay da jamiyyarsa ta NNDP gefe.
   A shekara ta 1937 kuwa sa’ar da Dr Nmandi Azikwe ya gamo karatunsa a Amurka har ya soma aikin jaridar ‘West African Pilot’ a Ghana, sai ya komo Nigeria. Anan suka haɗu da amininsa Oloye Davies wanda ya karanto Sharia a Ingila, suka shiga waccan jamiyya ta yarabawan lagos tare da ɗaukaka ta izuwa ‘Nigerian Youth Movement’. Suka haɗu da zaka-kuran mutane irinsu Ernest Sissie Ikoli, Samuel Akisan, James Churchil Vaughan, Kofo 
Abayumi da wasunsu suna ta rajin wayarwa ‘yan kasa kai ta hanyar rubuce-rubucen jaridu. Babbar maganar su itace “bamu yadda da mulkin mallaka ba, ‘yancin kai da dimokraɗiyya muke da bukata”.
   A haka aka tafi har wuraren shekara ta 1944 zamanin da  Sir. Arthur Richard ke shugabancin Nigeria, inda rikicin kabilanci ya raba Dr. Nnandi Azikwe a matsayin shi inyamiri da jamiyyar Yarabawa ta NYM, sai kurum yazo ya haɗu da Herbert macaulay suka cigaba a Jamiyyar Herbert ɗin a lokacin mai watau NNDP wadda ta sauya izuwa
 ‘National Council of Nigeria and the Cameroons (NCNC)’.
   Awannan lokaci, sai shugaban kasa Richard ya samar da sabon kundin tsarin mulki, wanda ya rage yawan zaɓaɓɓun ‘yan majalisa da wakilan ‘yan kasa ya kuma kara adadin ‘yan majalisar da-ba zaɓaɓɓu ba.
 Sai kuwa Dr Nnamdi Azikwe da Herbert macaulay suka shiga fafutukar yaki da wannan tsari. Suka shiga suka, suna bin yankuna suna wayar da kai da kuma neman tallafi domin tafiga zuwa Ingila suyi zanga-zangar nuna adawa da wannan kundin mulki a gaban majalisar kasar.
  Ana wannan rintsi ne Herbert Macaulay shugaban NCNC ya rasu, sai Dr Azikwe da yake matsayin akawu ya zama shugaba.
   A shekarar 1945 aka haramtawa Dr. Azikwe fitar da jaridarsa ta ‘Africa West Pilot’ bayan ta wallafa wasu zantuka dangane da yajin aiki a kasa wanda gwamnati tace basu da tushe balle makama. A shekarar 1947 kuwa aka sake zaɓen ‘yan majalisu, har kuma Dr. Nnamdi Azikwe ya zamo wakili zaɓaɓɓe a wannan majalisa ta lagos karkashin inuwar k’anwa jam’iyyar sa ta NCNC mai suna National Democratic Party (NDP).
   A shekarar 1951 kuwa sai sabon kundin tsarin mulki yazo daga Shugaban kasar lokacin mai suna John Stuart Macpherson, wanda ya tsinka wakilan Nigeria izuwa yankunan ta, ya kuma bada damar kowanne yanki ya zaɓi ‘yan majalisun sa a wata majalisa karama. Daga waɗancan majalisu  na yankuna ne za’a zaɓi wakili zuwa majalisar kasa.
   A lokacin, jam’iyyun NCNC da ‘Action Group’ ne suka fi samun tagomashi.
  Ita jam’iyyar ‘Action Group’ ta yarbawa ce wadda Chief Awolowo ke shugabanta, kuma ya zamo zaɓaɓɓen wakili a karkashinta. Jam’iyyar tana da goyon bayan rusasshiyar jamiyyar ‘Northern Youth Forum’ (NYF) ne mai adawa da Dr. Azikwe.
   Shi kuwa Dr. Nnamdi Azikwe  ya samu cin zaɓen yanki a majalisar kudanci karkashin jam’iyyar tasa NCNC, amma sai dai Chief Awolowo na Action Group ne mutumin daya fishi samun tagomashi a majalisar, don haka shine ya samu damar tafiya babbar majalisar kasa..
   Wannan kusan shine a takaice yadda siyasa ta faro a kudancin Nigeria kenan, saura muji yadda ta kasance a yankin Arewa.

Daga Bashir Tukur Gwarzo
Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »