Matsalar Zubar Jini Ga Mata

0 425

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Matslar zubar jini da ke samun mata wanda yake wuce qima a lokacin al’ada ko ba lokacinta ba, sakamakon matsalar  FIBROID ko PCOS ko waninsu to ga mafita nan da yardar ALLAH.

Wannan abinda zan fada ba wai magance Fibroid ko Pcos yakeyi ba, sai dai yana taimakawa ne wajan tsayar da jinin da yake zuba wanda yake wuce qima ko al’adar da take wuce lokacinta wani lokacin sai an garzaya asibiti.

ME YAKAMATA AYI?

A samu ganyen miyar Ewedu ( da yoruba) Ayoyo ( da hausa) mai dan yawa kadan, a wanke shi da kyau a tsaftace shi sosai, sai a markade shi a tace sai a sanya ruwan a cikin wata container a wuri mai mara zafi sosai.

Sai a rika dibar ruwan Ewedun na kimanin kwatan 1/3 kofi daya, sai a zuba ruwan zafi a ciki, a kada shi kafin a sha, a sha sau biyu a yini safe da dare.

Wannan hadin kuma yana da amfani ga masu matsalar Asthma, yana bayar da kariya ga harin farmakin cutar Asthma.

Wannan hadin yana da kyau ga wadanda ke son su rage matsayin sinadarin Cholesterol a jikinsu wanda sinadarin ke iya yin sanadiyyar haifar da ciwon zuciya (masu bukatar ragewa sai su kara da ruwan lemon tsami a cikin hadin, su rika sha Sa’adu da dare).

IN SHA ALLAHU za a samu lafiya, Allah yasa mudace.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »