An Koya Min Darasi {01} Labarin Wata Matar Aure Da Shaidan Ya Kaita Ya Baro.
AN KOYA MIN DARASI {01}
Tace…:
Muna zaman lafiya da shi da yan uwansa gaba dayanmu, babu abinda ya rage ni da shi daga ci, sha, sutura da wadataccen muhalli, yana matukar girmamani yana mutuntani sosai sannan yana kyautatamin yadda yakamata.
Sai watannin bayan nan ina zaune ni kadai sai na shiga wani tunani ina cewa zuciyata: kamar fa nan gaba zai iya karo min kishiya, sai kawai na shiga tunanin yadda za ayi na daqile wannan al’amari idan ma har da gaske ne zai iya faruwa.
Wata rana sai na shiga wani group din mu a WhatsApp naga ana tallan wasu abubuwa kamar haka: Zobe, Humra, da wasu layu da sauransu, akace wai na Mallakar miji da uwar miji ne kuma sai abinda nace ne zai rika faruwa a gidan.
Sai kawai na kwasa da yawa, ban duba tsadar da suke da shi ba. Naje gida nayita amfani da su.
Na kare maka bayani yanzu dai duk wata kyautatawar da yake min ta juye ta koma wulakanci, soyayarsa gare ni ta koma kiyayya, Danginsa sun tsane ni haka kurum. wallahy ina cikin mawuyacin hali yanzun nan, kuma ga shi aure zai kara a wannan watan. Na yi nadama sosai.
DARASI…
Abin da ta gujewa faruwarsa a farko yanzu kuma ga shinan zai faru ba makawa. Shin kuna ganin kuwa anya ba Shedan ne yazo mata cikin tunaninta har ya bata mugunyar Shawarar nan ba?
To ya kamata kusani cewa: Shedan babban makiyinmu ne, kuma mu rike shi a matsayin makiyinmu kar mu kuskura mu bashi wata dama domin hallakar da mu zaiyi
Yanzu ga shinan ta shiga halin da na sani, kuma yau ko gobe za a iya sakinta, ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko.
Gani ga wane…..
Allah yakara tsare mana imaninmu.
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com