Taƙaitaccen Tarihin Jaruma Amina Uba Hassan tsohuwar mata ga jarumin Kannywood Adam A. Zango.

0 605

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An haifi Amina Uba Hassan a garin Kaduna Najeriya inda Tayi karatun ta na gaba da Primary ma’ana Secondary a Makarantar Queen Amina College Kaduna daga nan ta wuce Polytechnic Kaduna inda taci gaba da karatunda na gaba da Secondary,

Sannan wasu suna kiranta da suna maman Haidar, inda ta bayyana cewa wannan sunan na maman Haidar ta samo shi ne sakamakon sunan Yaron ta mai wannan suna (Haidar)

SHIGARTA HARKAN FILM
A tattaunawan da manema labarai sukai da ita ta bayyana cewa tun tana karamar yarinya tana da sha’awar Harkar fina fina Hausa sosai wanda hakan yasa kullum a gida ana kunna musu fim suna kallo hakan yasa abin yake burgeta duk da a wannan tsawon lokaci Allah baiyi zamanta Jarumar ba sai yanzu da Allah ya kawo lokaci

Sannan ta bayyana wasu shirye-shirye wanda ta fito a ciki inda ta fara da Wani fim na Sani Musa Danja Wanda aka yishi a Kaduna mai suna Mai Shayi duk da a wannan fim special affair tayi (fitowa na musamman) sai fim din Gidan Danja wanda shine fim ɗin da mafi akasarin mutane suka santa sosai sai wani fim na kamfanin 2 Effect.

ABINDA TAFI SO
A tattaunawar ta bayyana ma manema labarai cewa abinda tafi so bai wuce yaron taba wanda shine Haidar.

ABINTA TAFI TSANA
Sannan ta bayyana KAZAFI a matsayi. abinda tafi tsana a rayiwar ta.

BURINTA A HARKAN FILM
Babban burita a harkar fim shi ne na zama Director wata rana cewar Jaruma Amina uba Hassan.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »