Wasu Daga Cikin Amfanin Busasshen Lemon Tsami

0 863

DAGA CIKIN AMFANIN BUSASSHEN LEMON TSAMI

1- Yana rage kitsen dake jikin mutum.

2- Yana da matukar amfani ga matsalolin zuciya.

3- yana taimakawa wajan kawar da tsakuwar dake cikin QODA “KIDNEY STONES” ( wannan mujarrabi ne ga masu matsalar QODA cikin Ikon ALLAH).

YADDA AKE BUSAR DA LEMON TSAMIN

Za ka samo Lemon tsami guda 4 manya kuma lafuyayyu, bayan an tsaftace su sosai sai a yayyanka su a kwance ( kamar duk guda daya a yanka shi gida 4 ko 5) ba tare da an cire bawon jikinsa ba, sai a shanya shi a wuri mai tsafta inda iska ke shigowa ba a cikin rana ba, da daddare ko da yamma za a shanya shi, sai a barshi har gari ya waye.

Kuma yakasance an rarraba su a lokacin shanyawar ba tare da daya ya hau kan daya ba.

YADDA AKE AMFANI DA SHI:

Bayan sun bushe ne sai a sanya su a cikin butar shayi ko dai wata karamar tukunya, a zuba kofi 4 na ruwa a ciki sai a dora akan wuta a barshi har tsawon mintuna 2 ko 3 ko 4 ( aya danganta da yanayin zafin abin girkin). Sai a sauke shi abarshi ya huce daidai sha, sai a rika shan kofi 1 da safe bayan sallar Asubah kafin a yi karin kumallo, sai kofi 1 kuma kafin sallar Isha’i ( “Amma ya zama dole ne mutum ya kauracewa duk wani abinci bayan ya ci abincin rana har zuwa bayan magriba kafin yasha maganin”.)

Wannan hadin kam mujarrabi ne musamman ma ga wadanda ke da matsalar tsakuwar dake cikin QODA ( KIDNEY STONES) da yardar Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »