Bareerah: Wallahy kuwa yar uwa sai dai muyi ta Addu’ar ALLAH yayi mana zabin mazan aure mafi Alkhairi a rayuwar mu, domin ni ganau ce ba jiyau ba, saboda hakan ya taba faruwa ne da wata makobciyar mu abin wallahi shiyasa nake ta jin tsoron auren wanda bai da Addini.
Labeeba: Allah sarki, ai kam dole ki saduda saboda ance : Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Malamar taci gaba da cewa: Kuma bayan mutum Allah ya ba shi aboki ko abokiyar zaman aure na kwarai to sai kuma ya rika bin qa’idojin da Addinin Islama ya gindaya masa a gidansa wajan sauke hakkokin iyalansa da kuma tabbatar da yiwa ALLAH biyayya da kauracewa aikata duk abinda ALLAH ya hana aikatawa.
Malama ta kara da cewa: Kuma dole ne ma’aurata sai sun tabbatar a duk lokacin da zasu kusanci junansu suna yin Addu’ar nan da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya horar da mu akanta, domin samun kariyar ALLAH ya kare mu kuma ya tsare mu da jaririn da za a samu rabonsa daga sharrin Shedanu.
Mai gabatarwa: Shin Malama akwai kebantacciyar Addu’a ne da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar a yayin da ma’aurata za su kusanci junansu ko kuwa duk Addu’ar da mutum yaga dama ne zai iya yinta?
Malama: Allah sarki, akwai mana ai babu wani abu mai amfani wanda zai amfane mu a rayuwarmu ta yau da kullum kuma yayi mana amfani a lahira wanda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama bai nuna mana ita ba, kuma babu wani sharrin da zai cutar da mu da rayuwar mu wanda bai nuna mana shi duk domin mu guje masa ba.
Mai gabatarwa: To Mallama gaskiya ya kamata a koya mana Addu’ar nan saboda ina kyautata zaton cewa da yawan wadanda mukazo wannan muhadarar maza da mata ba lallaine dukkaninmu mun iya karanta ta ba.
Kuma ya kamata a fadi muhimmancinta da amfaninta domin wasu sun iya amma ba sa karantawa a yayin da za su kusanci iyalinsu, ka ga idan suka ji muhimmancinta na tabbata za su rika karanta ta a ko da yaushe insha ALLAH.
(Insha ALLAH za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com