Aisha Talba (Kashi na 4 Hausa Novel)

1 62

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

AISHA TALBA (Kashi Na 4)


Tunda nashiga daki kaina ya hau saraman domin kuwa tun daga faruwan wannan abun naji jikina ba dadi, dakyar natashi nashiga bandaki nayi wanka hade dayin alwala nazo nayi sallar Azafar dina na kwanta ko abinci ban samu naci ba har aka kira la’asar sannan nayi sallata nakoma na kwanta tunane tunane kawai nakeyi,

can daga sama sama sai naji hon din mota da alamu Salmah ce ta dawo, banyi minti biyu dajin sautin hon din motar ba sai jinai ta turo kofar dakina tashigo Ta dago kanta ta kalleni nima kallon nata nayi naga jikinta duk ya mutu sai ta tashi ta zauna ta kalleni ta ce,” “Maza sukan fara fushi da kannansu ba gaira ba dalili shin maye ra’ayinka akan wannan maganar? yaya nah,”

Nayi shuru bance uffan ba, ta juyo kaina tana facing dina ta “Yayana kafada man me nayi maka domin shurun nan da kakeyi dani wllh jinake kamar ina mutuwa ina dawowa ne,”


Wasu hawaye suka gangaro a kuncinta masu dumi na kalleta cikin fuskar tausayi domin tadamu sosai nasa hannu nagoge mata hawayen na ce,” “Kada kidamu bakece silar 6acin raina va kuma 6acin randa nake bazan saukesa akanki ba,” ta kara gyara zama ta ce,” “To yanzu fada man damuwarka yayana,” na kwashe duk labarin abinda ya faru na fada mata tun farkon haduwarmu a facebook har fara ganin juna damukai har aron motoci danayi duk na fada mata amma abun mamaki ga abinda Salmah ta ce,” “Wllh yaya kayi babban kuskure da farkon haduwarku kafara mata karya baka tunanin nan gaba Allah ya kara hadu kushaku sai kuma ka gabatar mata da Yaya Sameer a matsayin abokinka?


me kake tunanin zai faru? to tunanin da zatai aranta cewa badan Allah kake sonta ba kashigo rayuwarta da karya don kasameta daga karshe bayan kasamu dukiya sai ka gujeta koh?

na fiddo ido domin kuwa ni kaina banyi tunanin haka ba, kaji yarinya me tunanin manyan mutane, na kalli salmah na ce,” “Ayya kanwata banyi tunanin dake kikai ba kuma babban kuskure na shine karyar da nayi mata amma kuma danasani keya ce,”
Salmah tace “Yaya bari naje na yi sallar la’asar,” tana fadar haka ta fita, ni kaina inajin dadin zama da kanwar nan tawa, Bani da wata babbar kawa ko aboki daya wuce kanwata domin kusan kowane sirrina tasansa kuma idan abu ya faru dani itace takan fara sani kafin wani yasani muddin ina gida to baka rabumu tare don kowane time idan ba aiki take ba to muna tare,”

Salmah bayan ta gama sallarta sannan ta zauna saman gado tana tunani a cikin zuciyarta ta ce,” “Dolane inje gidan su ‘yar iskar Aishar nan wadda taciwa yaya mutunci na kulla Abota da ita ko nasamu tazo gidan nan don hakama yanzu ya kamata nafara hada mata tarko barama naje gidansu yanzu,”
tana gama wannan tunanin ta mike ta janyo gyalenta ta shigo dakina ta ce,” “Yaya bani key din Marsendes 4matic dinnan zanje wani gu,”
na kalleta na ce,” “Kije a motar da kika dawo yanzu mana,”
ta dan ta6e baki ta ce,” “To ai babu mai acikinta badadewa fa zanyi ba,”

Na bude loka naciro mabudin na mika mata ta amsa ta fita tare da man bye bye,”

Zamuci gaba a part 5 gobe in Allah ya kaimu

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Yusuf muazu says

    Wow labari na dadi

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »