AISHA TALBA (PART 3)
Cikin 6acin rai najuya nakai hannuna zan bude marfin mota Sameer yayi saurin kai hannunsa ga marfin motar ya zageta nashiga na zauna mutanan nawa kowa yashiga motar daya tuko a 70 muka fita cikin wannan makaranta kawayenta sai kallonmu suke hadda juyowa nima naga hakane ta mirro ita kau ko wai gowa batayi ba, tatsaya gyam kamar wata dutse wasu tagwayen hawaye suka gangaro mata akan fuska, an kasa wadda zata tambayeta damuwarta acikin kawayenta saboda gudun 6acin ranta,
Sai aka samu wata daga cikin kawayen nata da Aisha take jinta kuma tasan yarinyar bata da tsoro wajen fadawa Aisha Gaskiya koda kuwa ranta zai 6ace ne ita kanta tana jindadin zama da ita sunanta Ikilima,
Ikilima ta kalleta cikin takaici domin kuwa sunji haushin wulakancin datayi man ta dan harareta ta ce,” “To maye kuma na zubar da hawaye bayan kin fada masa abinda ke ranki hmmm ai kin bamu mamaki gaye iya gaye hadadde duk da cewa ba fari bane sosai irin naki amma baza’akirasa baki ba ga gashin gira masu yawa gashin kansa kuwa ya kwanta liplip gashi Handsome guy kuma yana da dan tsayinsa don dakadan zai fiki tsayi kuma ya iya wanka ga la66a kamar tupper kuma……..,”
“YA ISA, Aisha ce ta dakatar da ita da hannu, taci gaba da cewa,” “Yabon nasa ya isa hakanan ko angaya miki bana sonsa ne to bari nafada miki ina mahau kacin sonsa kawai wasa nake masa amma yayi fishi ya tafi gashi ban san inda zan samesa ba kuma nasan bazai kara daga wayata ba amma dole kugano man gidansu muje, kuka yaci karfinta Ikilima ta kama hannunta suka sata a mota suka tafi,”
.
Zuciyata tafar fasa take domin ban ta6a jin irin kalaman da Aisha tazo man dasu ba,”
a kofar gida muka tsaya na bude marfin mota nafito suma abokanan tafiyar namu suka fito na kalli Sameer na ce,” “Sameer kuje kumaida masu motocinsu ba’a bina bashi koh?
Sameer ya ce,” “Eh KUDANCY ba abinka,” Na ce,” “Okey to Sai mun hadu Nayi masauran abokanansa godiya sosai domin naji dadin abinda sukai man, suka shiga mota suka wuce, Wasu tagwayen hawaye suka hau gudana a fuskata na tura gate nashiga adaidai wannan time din dana shiga naci karo da Salmah zata fita a mota Kiran Honda V6 jajir tunda naganta nayi saurin goge hawayen dake ambaliya a fuskata tazo kusa dani tadan tsaya ta sauke gilas a hankali ta kalleni ta ce,” “Yaya Sannu da dawowa, na kalleta na ce,” “Yawwa kanwa Ina zuwa?
ta ce,” “Kawai zan fita yawo ne naga nikadaice agidan,”
na dan fiddo ido na ce,” “To ina su mummy suka je,?”
Salmah ta ce,” “Sun wuce Yola dazu dazun nan bayan fitarka,”
“Amma ai da gobe ne tafiyar tasu kuma sai su tafi yau kuma ba’a sanar dani ba,” Salmah ta ce,” “Nima ban san dalilin tafiyarsu yau din ba amma daddy yana ta kiranka awaya baya zuwa line busy sai suka wuce amma yabar ATM dinsa yace nabaka shiya tafi da dayan kuma ya ce kada kafitar da kudi batare daya sani ba dole ka kirasa awaya idan zaka cira kudi,” Na sauke nunfashi na ce,” “Jeki adawo lafiya,” tayi murmushi ta ce,” “Allah yasa,”
ta wuce ni kuma acikin zuciyata na ce,” “Ameeeeeen,”
Zamuci gaba a part 4 gobe in allah ya kaimu.
Ab Kudancy