Aisha Talba (Kashi na 2 Hausa Novel)

0 84

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

AISHA TALBA PART 2

Ba muyi minti bakwai da zuwa ba sai ganin wasu motoci mukayi Morano Guda bakwai bakake sunshigo cikin wannan makaranta kallon motocin nan kawai nakeyi har saida sukayi parking daga can side guda sai jinai hanjin cikin sun fara kadawa nakasa fitowa nima ina jira ta fara fitowa,

Kwatsam sai ga calling dinta ya shigo wayata na yi picking na karata akunne tare da cewa,” “Hello gimbiya ta tun dazu nake ta jiranki amma shuru kodai nakoma gida ne?
“Wani irin kakoma gidan bayan nima nashigo wurin kaine cikin Marsendes din dake parke a gun? na ce,” “Eh nine to ki fito mana?

“A’a kai kafara zuwa kuma kai yakamata kafara fitowa don haka kafito kawai,” tana gama fadar haka ta kashe wayarta na kalli Sameer wanda dama shine ya tuko motar danake ciki na ce masa,” “Sameer fita da saurin ka bude man kofa,” Cikin sauri ya fito yazo saitin danake ya bude kofar na ziro kafafuwa na kasa cikin kasaita nafito cikin motar sameer yayi saurin kulle marfin motar ya tsaya bayana ya dan sunkuyar da kansa kasa sauran abokanan nasa suka fito sukayi cirko cirko a bayana abun nikaina ya bani sha’awa,”

Minti daya da fito wana sai wani security dayake cikin motar dake gaba da wadda take ciki ya fito cikin bakaken kaya yazo saitin kofar motar da take ciki ya bude mata kofa ya koma gefe suma sauran security duk sun fito sunzo sun tsaya gefe da gefen kofar motar da take ciki can sai ga wasu fararen mata kyawawa masu kyau hadaddu su biyar sunfito daga motocin dake gaba da bayan tata, suma sunzo suntsaya kamar yadda security sukai, ni dai nasaka namujiya ina kallon kofar motar da take abude wadda har yanzu banga kowa ya fito daga cikinta ba,

can sai gani nayi an sakko da kafa daya daga cikin wannan motar kafar dauke take da kunshi ja mai kyan tsiya, lokaci guda nashiga tunanin wannan kafar Wllh da ace zan samu wannan yarinyar amatsayin matar aure to da duk daren duniya idan mukazo kwanciya saina lashe kafarta sau 99 kafin nabata hakkinta na aure, can sai hankalina yadawo jikina naci gaba da kallon wannan kafar can saiga Aisha Talba ta bayyana surar jikinta afili ma’ana tafito gabaki daya daga wannan motar, na kalleta sosai fuskarta babu bille sai falli take taji kyau idan kaganta farace sol kamar balarabiya tana da tsayin hanci bakinta cas dan daidai dauke da jambaki idanuwanta kuma manya duke da tozali sannan tana da dan tsayi amma ba sosai ba,

Na kalleta ta kalleni sannan ta tunkaro inda muke tsaye da murmushi takeyi amma kuma sai daga baya naga ta murtuke fuska sai kace nayi mata babban laifin ganin yadda naga tana kallo na,” Ba tare da nakalli Sameer ba na ce,” “Kai Sameer ya naga tana tunkaromu ne da fuskar mazga kai wllh inah mushiga mota mutafi kawai, sameer ya ce,” “A’a Allah ya kyauta ka kwarara zuciyarka ka dake karkaji tsoron yi mata magana,” bakowa zai gane magana mukeyi ba amma su abokanan tafiyarmu sunji komai,”
.
Cikin kasaita da rangwada suka karaso inda muke, wani kallo data wurgaman wllh sai da naji dama marina tayi tsabar furgici ta kai minti biyu tana kallon dressing dina sannan ta kalli fuskata ta ce,” “Wow Alhaji Abdulrazaq Ahmad ( Ab kudancy ) koh? Na kalli kwayar idanuwanta na ce,” “Eh,”


Ta 6ata rai ta ce,” “Aikin banza an fada maka kaburge nine shine ka kakwaso wadan nan kazaman kun zo wai don kaburgeni koh? to bara nafada maka sam bakayi man ba Idiot hmm kasan me? Raina ya 6ace domin banyi tsammanin haka daga gareta ba nadakatar da ita daga cigaba da maganarta na ce,” “Ya isa haka domin bazan juri jin wannan kalaman naki ba amma ina so kisani wllh da ace wata ce ta fada man irin kalaman da kikai man yanzu wllh da sai na yage mata harshe don haka sai anjima duniya ai ba gidanmu bane kema bana babanki bane Na barki lafiya,”

hhhh Guys ku biyo ni a part 3 kuji abin mamaki

Zamuci gaba a part 3 gobe in allah ya kaimu.


Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »