Yadda Zaa Magance Ko Rage Cutar Asthma.

0 494

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ZUWA GA MASU FAMA DA CUTAR ATHSMA ( ASMA)

Cutar Athsma itama daya ce daga cikin sauran cututtukan numfashi wadanda yara da manya ke fama da ita.

Abinda mai fama da cutar Athsma yakamata ya nema saboda samjn saukinta ko ma rabuwa da ita gaba data cikin iko/da yardar Allah su ne kamar haka:

1- Zuma

2- Garin sassaken marke

3- Tafarnuwa( a markada ta)

5- Garin Citta

6- Garin Habbatus saudah.

Sai a kwaba su wuri guda suyi kauri sosai (amma a sanya zumar da dan yawa), sai a rika dibar cokali 2 ana sanyawa a ruwan dumi Kofi 1 madaidaicin Kofi, ana sha safe da rana da daddare, kuma a rika lasar mai kaurin akai-akai, adau kamar tsawon sati 2 ana amfani da ita sai aje aga likita.

Karamin yaro kuma idan ya fara cin abinci sai arika bashi karamin cokali ( wacce aka sirka da ruwan dumin, kuma ana lasa masa mai kaurin kadan kadan a bakinsa), Idan kuma bai fara cin abinci ba sai a rika lasa masa kadan a bakinsa kuma idan ana shayar da su sai itama uwar ta rika shan hadin manyan da yake a sama.

Insha Allahu za Ku samu natija a wannan hadin.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »