Bani Da Lafiya Kashi Na sittin (60)

0 29

ABIN LURA

“Tabbas BOKA dabam MALLAM ma dabam, kamanninsu sunyi hannun riga kwatakwata babu wani hadi na kusa ko na nesa, duk wanda yace muku ya san abinda zai faru anan gaba ko yake nuna zai iyayin wani abinda Allah ne kadai zai iya yi to ba makawa BOKANE wannan ba MALLAM ba. Ya zama wajibi ku kaurace masa. Yanzu sun zama BOKAYEN zamani suna da Ofisoshin da suke aiwatar da bokancinsu a birane sun baro dazuka da kauyuka wadanda wasu kidimammun ke kiransu da MALAMAI.

Bareerah taga wannan matar ta zo wurin da ake bukatar tazo sai tace: Alhamdulillah, ai kam ina so ayimin wannan tambayar saboda mutane da dama sun kasa bambance tsakanin Malami da kuma boka.

Labeeba: Maasha Allah , gaskiya kam ya kamata a ceto ta daga cikin gwalalon Maman Sultan.da kuma sauran mutanen da suke kasa raba tsakanin Mallam da BOKA.

Bareerah ta dafa kafadar matar sai take cewa: Wato Yar uwa, sanin Kanki ne Allah shi ne kadai Ubangiji, mahalicci kuma mai iko akan kowa da komai sannan na tabbata SHI kadai ne kike da sanin mai sanya cuta kuma mai bayar da waraka, shi ne mai kashewa kuma mai rayawa, mai bayarwa kuma mai hanawa ko kuwa?

Matar: Tabbas kuwa imani da haka had cikin zuciyata, ai matukar dai mutum musulmi ne shi to ya zama wajibinsa ne ya yarda da wadan nan bayanan ko kuma ya warware musuluncinsa da Imaninsa.

Bareerah: Maasha Allah, Wato a irin wannan yanayin akwai wasu mutane kala 3 wadanda ke bugar kirji suna nuna su ma suna da sanin jiya da anjima da kuma gobe kuma suna ganin za su iya tabbatar da duk abubuwan nan sa Na lissafo miki su a sama, abinda Allah ne kadai ke da ikon tabbatarwa ko kin tabbatarwa.

Matar: Ikon Allah, to Yar uwa suwanene kuma wadan nan haka?

(Insha Allahu a rubutu nagaba za muji ko suwanene.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »