Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin Da Tara (59)

0 519

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Ku rika lura da wadanda za ku rika neman shawara akan wasu damuwoyinku, saboda an hallakar da yawa daga cikin mutane a sanadin rashin dacewa da abokan shawara, wasu sunyi asarar Imaninsu wasu kuma sunyi asarar jin dadinsu na yau da gobe a karshe kuma suka tashi cikin hasararru.”

Matar tace : Ai kam sai dai kar a Kuma, domin har nima tace min ina da aure ne? Nace mata eh ina da shi har ma da yara 3, amma kalau muke tare da miji na ba abinda narasa kuma babu wata matsala a tsakaninmu Alhamdulillah.

Bareerah: Allah sarki, Allah yasa mudace.

Matar : Ai kam budar bakinta kenan sai cewa tayi: Tab dijam..! Ai da sauranki domin dole ne sai kin tashi tsaye ke ma kin nemi maganin da za ki mallakeshi saboda yanzu mazan ne sai ahankali ba su da tabbas sai ana yi musu irin haka ko ki zama baiwa.

Labeeba: Subhanallah, Bareerah kinji mutuniyar ko? Gaskiya wallahy tana batar da mutane dayawa, Allah yakara tsare mana imaninmu.

Bareerah: Ameen ya Rabb. To ke baiwar Allah daga nan kuma ya kukayi da ita kenan?

Matar: Ai muna cikin tattaunawar ne sai muka hango ita Labeeba ta shigo makaranta, sai muka biyota domin muga wacece ita, domin ita Maman sultan din ma da niyyar fada tazo amma yanzu an kira ta a waya tana nan dawowa nan ba da jimawa ba.

Bareerah: Ikom Allah..! Niyyar fada kuma? To ke Labeeba me ya hadaku ne da ita haka har take nemanki da fada haka?

Labeeba: Ai dole ne taji ba dadi, domin tana cikin gina harkar bokancinta ne sai ni da direban muke kokarin rushewa, taga dai asirinta zai tonu sai ta fice daga motar tana ta bankamana ashariya.

Matar: Wai ku tsaya ! Ni fa kun raba min hankali… “Wai ancewa raggo : Ci abinci ka tafi gona”. Me nene illar ita Maman sultan din nanne, saboda ita malami take cemin amma kuma ku kuna cewa Bokaye, ina so ku fayyacemin bambanci tsakanin Malami da kuma Boka.

(Insha ALLAHU a rubutu nagaba za muji abinda suka labarta mata.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »