Tarihin Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli

0 1,064

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

AMB. Ahmed Nuhu Bamalli an haife shi a ranar 8 ga watan Yuni shekarar alif 1966, lauya ne, ma’aikacin banki kuma jami’in diflomasiyya.

Shi ne tsohon jakadan Najeriya a ƙasar Thailand tare da amincewar kasar Myanmar a lokaci guda, kuma Sarkin Fulani na Zazzau na 19 a yanzu, Shi ne sarki na farko daga gidan sarautar Mallawa da aka nada a karni guda bayan rasuwar kakansa, Sarki Alu Dan Sidi a shekara ta alif 1920.

An haifi Bamalli a garin Kwarbai Zaria, jihar Kaduna. Shi ne ɗan farko ga Nuhu Bamalli wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin wajen Najeriya.

Ya samu digiri (LLB) a fannin shari’a a shekarar alif 1989 daga Jami’ar Ahmadu Bello, sannan kuma ya yi digirinsa na biyu a fannin harkokin kasa da kasa da diflomasiyya a jami’ar a shekarar alif 2002.

Yayi PGD dinsa fannin gudanarwa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu a shekarar alif 1998.

Ya kuma halarci taron hadin gwiwa kan magance rikice-rikice a Jami’ar York a shekarar 2009 kuma ya kammala difloma a kan jagoranci kungiya daga Jami’ar Oxford a shekarar 2015.

Bamalli ya yi aiki da Hukumar Kula da Birane kafin ya zama shugaban ma’aikata a Mtel, bangaren sadarwar wayar salula na tsohuwar Kamfanin Sadarwar Najeriya.

Ya kasance kwamishina na dindindin a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna a shekarar 2015. Har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai ne ya nada shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau a ranar 7 ga watan Oktoba shekarar 2020. Shi ne dan Nuhu Bamalli (Magajin Garin Zazzau) na farko.

Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan sarautar Mallawa cikin shekaru 100, bayan rasuwar Alh Shehu Idris.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »