Shaaban Ibrahim Sharada ɗan siyasa ne a Najeriya kuma ɗan jarida daga jihar Kano wanda ya kasance mataimaki na musamman ga shugaba Muhammad Buhari kafin ya zama ɗan majalisar wakilai a 2019.
RAYUWAR SA
An haifi Sha’aban ne a ranar 1 ga watan Janairun shekarar alif 1982 a unguwar Sharada da ke karamar hukumar Kano, ya halarci makarantar firamare ta Salamta, sannan ya halarci Sakandaren Gwamnati ta Sharada. Ya yi Digiri na 1 a Mass Communication a Jami’ar Bayero Kano.
AIKIN JARIDAR SA
Sha’aban ya fara aiki ne a matsayin mataimaki na kasuwanci a Freedom Radio da ke jihar Kano har zuwa lokacin da ya zama mataimaki na musamman ga shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari.
SIYASA
Sha’aban ya fara harkar siyasa ne a shekarar 2009 a lokacin da yake karatun digiri na farko, inda ya tsaya takarar Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Dalibai ta kasa reshen Jihar Kano, kuma an nada shi a matsayin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Tarayyar Najeriya, Muhammad Buhari. a shekarar 2016
An zabi Sha’aban Memba a babban zaben Najeriya na 2019 don wakiltar mazabar Kano Municipal a majalisar wakilai ta Najeriya.
A halin yanzu shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaro da Leken asiri.