Dayawa za kaga a kasar Hausa a lokocin da aka tabbatar da mutum yana karancin jini, ko tana dauke da juna biyu ko ta Haihu ta zubar da jini dayawa sai kaji ance shan maltina da madara, a fahimtar mutanen mu zai kara jini.
Gaskiyar magana babu alaka sakanin karin jini da Maltina da Peak milk, sabida wake kwara daya yafi Maltina da Peak milk wajen samar da sinadaran kara jini.
Idan kun duba jikin gwamgwanin peak milk za kuga babu sidaran karin jini a ciki ( not rich in iron) Haka Maltina ma Babu sinadaran kara jini a ciki.
Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk yazama maganin karin jini ?
Amsa: wannan kawai al’adace ta mutanen mu ba tareda sanin abun ba.
Maltina na dauke da sinadaran:
- Calories
- Carbohydrates
- Fat
- Vitamin
- No Iron
Peak milk na dauke da sinadaran:
- Fat
- Carbohydrates
- Protein
- Salt
- Vitamin A and D
- No Iron
Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana bukatar sinadaran iron daga abincin da muke amfani.
Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashe wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani da su wajen siyan abinci masu dauke da iron kamar :
- Wake
- kifi
- Nama
- kwai
- Kaza
- Fara
- zogole
- Cashew
- cavage
- salat
- Spinach
- da sauran su.
Allah ya kara mana lafiya gabaki daya.
Dr. Zaharaddeen
To mungode alh ya kara mana lfy da xama lfy
Amin