AMFANIN KABEJI GA LAFIYAR DAN ADAM

5 55,921
AMFANIN KABEJI GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM

Nasan cewa Mai karatu ya Riga yasan kabeji basai nayi wani bayani akan menen kabeji ba kasancewar mafiya yawan Hausawa suna amfani dashi a gidajensu KO wasu Su siya akan hanya sakamakon yadda muke dashi.
Kai tsaye bari nafara Allah yabada ikon fahimta Amin. 
1. RAGE KIBAR JIKI : 
Binciken masana ya tabbatar da cewa Kabeji yana rage wa wanda ke cinsa kiba. Don haka idan mutum ba ya so ya rika yin kibar wuce geji, ya lizimci cin kabeji.
2. YANA KARA KAIFIN BASIRA: 
Kabeji cike yake da sinadarin ‘Bitamin K’ wanda shi ke kara wa mutum hazakar kwakwalwa da kuma fahimta. Haka kuma masanan sun ce Kabeji yana taimakawa wurin yi wa mai amfani da shi garkuwa daga cututtukan da suka shafi kwakwalwa. 

A nan kuma sun ce, jan Kabeji ya fi Kore yin wannan aiki.

3. KARA WA MUTUM KYAU: 
Ganyen Kabeji yana da sinadarin da ke sa fatar mutum ta rika sheki da kyau, sannan yana sa taushi da kyallin gashi, haka ma farcen mutum kan yi kyau.
4. KABEJI NA CIRE DATTI DA WARIN JIKI: 
Masana sun tabbatar da cewa Kabeji na taimaka wa mutane wurin cire datti da warin jiki. Saboda sindarin ‘Bitamin C’ da ke cikinsa. 
Wanda yake garkuwa da wasu manyan cututtukan fata da kuma cututtukan sanyin kashi.
5. KABEJI NA MAGANI DA GARKUWA GA CUTAR KANSA:
Kabeji na zama garkuwa ga cutar Kansa, sannan kuma ya kan rage kaifin cutar ga wadanda su ke dauke da ita. 
Bincike ya tabbatar da cewa Mata masu dauke da cutar Kansar Nono, idan su ka lizimci cin Kabeji cutar ta kan yi musu sauki sosai.
6. KABEJI NA YIN MAGANIN HAWAN JINI: 
Ganyen Kabeji na taimakawa wurin bude jijiyoyin jini, ta yadda jinin ke samun daman bin jiki yadda ya kamata. Wannan lamarin na magance matsalar hawan jini.
7. KABEJI NA MAGANIN CIWON KAI: 
Busasshen ganyen Kabeji idan aka yi shayi da shi yana magance ciwon kai. Haka kuma idan aka matse ganyen a cikin tufafi a ka daura a kan mai ciwon kai, zai iya samun sauki. Ko kuma a matse ruwan a rika sha.
8. KABEJI NA RAGE YAWAN JIN KISHI: 
Ganyen Kabeji na taimakawa mutum wurin rage mishi yawan jin kishi. Idan mutum na mu’amala da ganyen Kabeji, zai kasance ya na shan ruwa ne kawai a lokutan da su ka dace ko kuma jikinshi ke bukatan ruwan.
9. KABEJI NA DAIDAITA SUGA: 
Ganyen Kabeji na daidaitawa mutum suga a jikinsa, ta yadda zai kiyaye mutum ga kamuwa da muguwar cutan suga.
Sai dai akwai irin cin da mutum zai rika yi wa ganyen Kabeji ya janyo mishi matsaloli. Cin Kabeji na wuce gona da iri na iya janyo cututtuka kamansu, ‘Flatuance’, ‘Diarrhea’ da kuma ‘Hypothyroidism’. 
Allah ya tsaremu baki daya amin. 
Kuyi kokarin tura aiyukan mu ta hanyar amfani da daya daga Cikin  social media dake kasa don mutane Su amfana
  1. Unknown says

    Aslm dan Allah inason afadamu sunan (aduwa) da turanci, sai kuma( taura).

  2. Unknown says

    Desert date

  3. Babangida Sani Yandadi says

    l appreciate this publication and want to be part of it.Keep it up

  4. rabiuw@gmail.com says

    Mungode

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »