Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shine Babban likitan duniya baki daya wanda har yanzu ilimin likitanci yana nan har yanzu ana amfani da shi har zuwa koyaushe.
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, yayi mana umarni da Shan Nonon Saniya domin akwai samun waraka acikinsa da yardar Allah.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
(Lallai Allah mai girma da buwaya,bai taba saukar da wata cutaba,face ya saukar da maganinta,sai da mutuwa,dan haka na kwadaitar da ku akan shan nonan Saniya,domin ita tana ci daga dukkan itaciyoyi)
@صححه الألباني في السلسلة الصحيحة -رقم:(518)
A wata Riwayar Manzon Allah ﷺ yana cewa;
(Ina kwadaitar da ku akan shan nonan saniya domin nonanta warakane,……kuma nayi maku kashedi daga Namanta,domin namanta akawai cuta)
@صححه الألباني في صحيح الجامع – رقم:(4061)
Malamai suna cewa dukkan abinda Manzon Allah ﷺ ya faɗa na magani tabbas haka yake babu kokwanto a cikinsa.
Amfanuwa daga wannan magani yana da alaqa da Imaninka da yardarka da gaskatawarka ga Manzon Allah ﷺ.
Allah Shine Mafi Sani