Amfani Da Fitsarin Rakumi Don Magance Cututtuka a Jikin Dan Adam

0 5,841

Akwai hujjoji da dama na kimiyya a da kuma na yanzu cewa fitsarin Rakumi yana da amfani wajen magance wasu cututtuka dake jikin dan adam.

Ibnu Seena yace mafi alfanun fitsarin shine fitsarin Raƙuman makiyayi waɗanda ake kira da Larabci Najeeb.

Fitsarin Raƙumi yana da tasiri wajen maganin cututtukan fata kamar Makero, Ƙyasbi, Ƙurajen jiki, Ƙuraje baki dana leɓe, gyabon hannu dana hammata. Hakanan yana da amfani wajen sanya gashi yawa, ƙyalli da kauri kuma yana hana da warkar da amosanin ka.

Gwaje-gwaje na Laboratory sun nuna cewa Fitsarin Rakumi na dauke da sinadarin potassium, sunadaran albuminous da kuma kaɗan na sinadarin uric acid, sodium da creatinine.

Wani Dokta mai suna Ahlaam Al Awadi, masanin kwayar cuta, ya tabbatar a kimiyance cewa za a iya amfani da Fitsarin Rakumi don maganin cututtukan fata kamar tautau, kumburin fata, ƙyasbi, wadanda shafani ya tayar musu da fata, kuraje, tabo dadai sauransu.

Haka kuma wani Dr. Mai suna Faten Abdul Rahman Khurshid yayi bincike kuma ya kammala da cewa Fitsarin Raƙumi na maganin kansa.
Sannan Journal of Cancer Science & Therapy sun shaida fitsarin raƙumi yana da sindaran kare kansa kuma ana iya amfani dashi don maganin kansar.

MAGANIN ANNABI (SAW)


An ruwaito daga Anas (ra) cewa: Yanayin Madina bai dace da wasu daga cikin mutanensa ba, don haka Annabi (SAW) ya umurce su da su ci gaba tare da makiyayan su, watau Raƙumansu , kuma su sha nononsu da fitsarinsu (a matsayin magani) “

A duba Saheeh Al Bukhaari – shafi 7, Hadisi na 5686.

Allah subhanahu wata’ala ya bada lafiya Amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »