LABARIN IYALIN DA FYADE YAI SANADIYYAR TARWATSEWAR SU

1 308

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Assalamu alaikum

Masoya na wannnan shafi na alummmar hausa wannan karon

munzo maku da wani dan takaitaccen labari ne wanda ya kasance tunatarwa a garemu gaba daya fatan allah ya amfanar damu da darsin dake cikin sa kuma yayi mana tsari daga aikata hali irin wannan

Wata mata ce tafita unguwa, Sai tabar yaranta uku a gida, namiji me kimanin 24 years da k’anwarsa me shekaru 15, sai k’aramar k’anwarsu me shekaru takwas a duniya.

Sai wan nan yayan nasu ya aiki k’aramar yarinyar nan waje me nisa, bayan ya tabbatar da yarinyar tayi nisa, sai yaje ya samu k’anwarsa me kimanin shekaru 15 kwance a d’aki.

Tana ganinsa a dakinta, sai tace yaya lafiya?

Sai yace, lafiya lau kanwata, taimakamin nake so kiyi kuma bana bukatar kowa yaji, sai tace, taimako kuma yaya? Shikuwa yace, “eh kanwata, saboda idan banyi ba ina tinanin mutuwa zanyi, haka dai ya dinga lallabar k’anwarsa.

amma sam bata aminceba, ganin yadda kalarsa ta canza babu tausayinta a fuskarsa, sai ta fara bashi hakuri kamar haka.

Dan Allah yaya kayi hak’uri, dan Allah yaya kayi hak’uri, ka taimakawa rayiwata, yaya mutuwa zanyi dan Allah yayi kayi min rai.

Haka K’ANWARSA ta dinga kuka tana bashi hak’uri, amma sai yace, ta daina kuka kar mak’otansu suji abinda yake faruwa, Amma duk da haka bata daina bashi hak’uriba, tayi iya k’ok’arinta ta kubuta daga gareshi, amma yaci k’arfinta, tare da kashe mata jikinta gaba d’aya, sai ya abkawa kanwarsa uwa daya uba daya.

Zafin ne ya rud”eta ta kuruma wani uban ihu sam ta daina motsi, numfashinta ya tsaya cak, amma duk da haka bai tsorata ba sai da buk’atarsa ta biya, ashe mak’otansu sunji ihun kanwar tashi, sai sukayi tinanin ko mamanta ce take dukanta.

Bayan ta farfado ne ya canza mata kaya, san nan ya canza mata zanin gadonta a sakamakon jini ya batashi, sai yazo gabanta ya durkusa yana taba hakuri tare da neman gafara da afuwarta. Allah sarki, ita kuwa hawaye sunki tsayawa, ta kasa dakatar da kanta daga zazzafan kuka, ko kallonsa bata sanyi.

Bayan mahaifiyarsu ta dawone ta tarar da yarta cikin mummunan hali, tace waye yayi miki wan nan cin zarafin har gida? Sai ta kara fashewa da kuka tace yayane.
Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, inji mahaifiyarsu, ina yayan naki yake yanzu? Tace bata san inda yakeba.
Babansu ya dawo aka gaya masa, ya nuna bakin ciki akan abinda ya faru matuk’a, a sanadin tsoron da yaran yaji sai ya gudu yabar unguwar, har saida maganar ta fito kowa yaji abinda ya faru.

Yarinyar da ita da kanwarta suka daina zuwa makaranta saboda nuna su da akeyi, ko waje suka daina fitowa domin kunya da kuma gudun tsokana da mutane sukeyi musu.
Dalilin haka ne yasa babansu ya siyar da gid

ansa da duk wasu kadarorinsa daya mallaka a garin ya tashi yabar garin gaba daya, domin yarsa ta samu farin ciki, tayi karatu cikin kwanciyar hankali, Allah ya kawo miji tayi aure.

Shikuma yayan nata babansa da kansa ya kamashi da hannunsa, ya kaishi wajen Hukuma domin ya girbi abinda ya shuka.

YA ALLAH KA TSARE MANA MATUNCINMU DA IMANINMU AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM
FYADE MASIFA CE, NEMI TSARI DAGA AIKATA LAIFI YAFI ALKHAIRIN AIBATA ME LAIFIN

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. ismail says

    ameem thumma ameen

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »