Ma’anar Alamomin Dake Jikin Tutar Rundunar Sojin Najeriya.

0 652

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga runduna wanda yawan su yakai 18,000 a bataliyar sojoji da rundunoni masu goyon baya a karshen yakin duniya na biyu a shekarar alib 1945, karfi da yawan Sojojin Najeriya ya karu zuwa kusan 126,000 a bangarori uku a karshen yakin basasan Najeriya a shekarar alib  1970.

Dangane da akida da kuma  aikin Sojojin Najeriya bai canza ba; aikinta ya kasance don rufewa da kuma fatattakar maƙiya.

Sojojin Najeriya suna amfani da tuta wacce take dauke da ratsi-ratsi guda uku a tsaye (JA, BAKI, da JA). A kansa alama ce ta Tsuntuswa (Mikiya), da Tauraro mai kaifi shida, da kuma Rubutun Larabci.

Alummarhausa tayi binciken alamomin da kuma ma’anar su. An daga tutar a Hedikwatar  tsaron Sojojin Najeriya, dake birnin  Abuja.

TSUNTSUWAR (MIKIYA)

Tana nuni da kyakkyawan karamci da kuma ƙarfin sojojin Najeriya. Kamar dai Mikiya, misali Sojojin Nijeriya suna sa ido sosai a ƙasar yayin lokutan zaman lafiya da kuma cikin shirin yaƙi.

TAURARUWA (MAI KAIFI SHIDA)

tauraruwa
Tauraruwa

Tauraruwa mai kaifi shida alama ce ta farko ta hadin kan Najeriya kuma Gwamna-Janar Lord Lugard ne ya fara buge su a shekarar 1914, shekarar hadewar Najeriya, don nuna yadda aka hada kawunan Arewa da na Kudancin da suka kafa kungiyar al’ummar da ba za ta rabu ba

Saboda haka, Sojojin Najeriya dole ne su kiyaye hadin kan kasar a kowane lokaci (shi ya sa Aguiyi-Ironsi ya fitar da Dokar Haɗuwa ta lamba 34 a ranar 24 ga watan Mayun, shekarar alib 1966).

RUBUTUN LARABCI.

Rubutun larabcin dake akan tambarin Sojojin Najeriya shine, “NASRUNMINALLAH” wanda yake nufin “NASARA TA ZO DAGA ALLAH KAWAI.” Kalamar taken tsohon shugaban jihadi ne, Uthman Dan Fodio, Shugaban Halifancin Sakkwato wanda Turawan Ingila suka rubuta a ƙarƙashin Lord Lugard.

LAUNIN JAN.

Wannan launi yana nunawa sojoji maƙiya, girke dasu, da ayyukansu.

BAKAN LAUNI.

Bakin launin yana nuna mahayan dawakai, masu sulke, da kuma ƙwararrun sojoji.

Wannan shine cikakken bayanin abubuwan dake jikin tutar rundunar sojin Najeriya, Muna fata idan anga kuskure a bayanin sai a sanar damu mu gyara.

Aƙarshe munaiwa Sojojin Najeriya fatan samun nasara akan maƙiya a kowanne lokaci Allah ya Albarkci ƙasar mu Nigeriya Amin.   

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »