TASIRIN HABBATUS-SAUDA GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM

0 373

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

1. KARIN MAHAIFA.

Abinda za ki yi anan shi ne ki samu man Habbatus-Sauda da zuma za ki hada awajen guda dai-dai yawan su ya zamo daya, sai ki zuba su a mazubi daya, za ki sha rabin cokali sau uku a rana.

*2. CIWON KAI MAI TSANANI

Ga mai fama da matsalolin ciwon kai sai ya samu man Habbatus-Sauda ya shafa a gaba goshin sa, sannan ya dan diga kadan a hanci, bayan ga haka ya kasance mai cin irin habbatus-Sauda bayan an gasa shi kadan tare da zuma, akalla sau biyu a kowace rana.

3. MURA DA SANYI

Ga mai fama da mura sai ya samu zuma su hada da Man Habbatus-Sauda, sai ya sha rabin cokali a kullum sannan su diga man kadan a cikin hanci.

4. TSURO A KAN FATA

Abinda za ka yi , shi ne sai ka nika irin kwayar Habbatus- sauda ,

sai ka kwaba da ruwa, sannan ka shafa akan wannan tsoron. Sau biyu a rana.

5. MATSAlOLIN DA SUKA SHAFI HANCI DA MAKOGWARO

Ga mai fama da irin wannan matsalolin, sai ya samu lemun tsami mai kyau, ya matse ruwan a kofi sannan ya zuba ruwan zafi sosai akai, rabin cokali na man habbatus- Sauda, sannan sai ya shaki wannan tiririn ruwan zafin. Haka zai yi sau biyu a rana.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »