Saratu Muhammad Gidado wacce akafi sani da (Daso), shaharariyar yar Wasan Hausa ce, wanda mafiya yawancin fina finanta takanfito ne a mahaifiya.
An haifi Daso a ranar 17 ga watan Janairun shekarar alib 1968, a Chiranchi dake karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Daso ta fara shirin fin din Hausa a masana’antar finan finan Hausa ta Kano a shekarar 2000 inda ta fara fitowa a cikin shirin fim din Linzami da Wuta wanda Kamfanin shirya fina finan Hausa na Sarauniya ya dauki nauyi.
A shekarar 2015 ne dai Daso, ta zama Magajiya ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II.