Wankan jego yana ɗaya daga cikin daɗaɗiyar al’adun da Hausawa kan yi, idan mace ta haihu.
Ana wankan jego ne domin riga-kafi daga wasu cututtuka da ka iya shiga jikin mai Jego. Haka kuma yana taimakawa wajen ƙara mata lafiyar jikinta ta hanyar tafiyar jini a jikin mai Jega da sauransu.
Akan tanadi sasaƙe da ganyaye da saiwoyi da kwatarniya ko baho da ƙatuwar tukunya ko garwa da ƙoƙo donyin wankan.
Akan tafasa ruwan wankan tare da waɗannan sasaƙen da ganyaye da saiwoyin a cikin ƙatuwar tukunyar.
Idan ruwan ya tafasa sosai, sai a kwashe a zuba cikin kwatarniya ko baho. Mai Jego za ta yi amfani da ganyen runhu ko na darbejiya wanda za ta riƙa tsomawa cikin ruwan zafin nan tana fyaɗawa a jikinta ma’ana zata tsoma ganyen cikin wannan ruwan zafi sauta dinga bugun jikinta dashi.
Haka za ta yi ta yi har ruwan ya ƙare a jikin baki daya.
A kanyi wankan jego ne na kimanin kwana arba’in ko wata biyu. Wannan ya danganci al’adun wurin da mai Jegon take.