Duk inda ka hadu da gungun mutane suna zaune ana ta yada zantuka ba birki, sannan baki kuma na ta motsawa, to ina tabbatar maka cewa ana shan rake a wannan wuri.
Ko da yake sau da yawa, akan dan daga wa mai shan rake kafa a bashi uzuri saboda ganin yakan shiga wani hali na zautuwa idan ba a taro shi ba musamman idan anyi dace da raken mai zakin gaske.
Sai dai kuma wani hanzarin ba gudu ba, rake na da matukar amfani a jikin mutum wanda da yawa ba su sani ba.
Ga amfanin da rake take yi a jikin mutum.
- Rake na kara karfin kashi domin tana dauke da sinadarin ‘Carbohydrates’.
- Rake na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido.
- Shan rake na kare mutum daga kamuwa da zazzabi musamman idan aka matso ruwan aka sha.
- Rake na hana lalacewan kumba,karyewa ko canza kala.
- Rake na sa rauni ya warke da wuri.
- Yana kuma taimakawa wajen samun kaifin kwakwalwa.
- Shan ruwan rake na taimakawa wajen kawar da warin baki da lalacewar hakora
- Shan rake na kwara da matsalar rashin haihuwa ga matan da ke fama da wannan matsalar, yana kuma bunkasa girman jinjiri a cikin uwar sa sannan yana hana mata masu ciki yin bari.
- Rake na taimaka wajen hana jiki ya nuna tsufa da wuri.
