Yadda Zaki Hada Tomato in Egg

0 432

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wannan hadi da zan koya miki zai tashi kamar yadda ake wainar kwai amma kuma ita za’a sanya tumatir a cikinta.

KAYAN HADI:

  • Tumatir yadda kike so.
  • Kwai yadda kike so.
  • Mai.
  • Gishiri.
  • Magi.

YADDA ZAKI HADA:

Photo by Pixabay


Da farko zaki samu tumatir dinki masu kyan gaske kuma manya bawanda yake da ruwa a ciki ba.

Saiki wanke bayansa, sai kuma ki yanka su sala-sala, bayan kin gama yanka su saiki dauko kaskonki ki sanyashi a wuta saiki kawo mai ki zuba a ciki.

Idan maidin ya toyu saiki kawo wannan tumatir dakika yanka sala-sala saki sanya shi daya bayan daya a cikin wanan mai din, saiki kawo gishiri kadan ki dan barbada a kansa,.

Baya kin lura da cewa yadan soyu saiki fasa kwanki ki kadashi ya kadu sosai kisa magi da dan gishiri, kada kisa gishirin da yawa saboda kinsan cewa tumatir din da kika sa shima kinsa gishiri, kinga a kwan da kika fasa idan kika sa gishiri da yawa zai yi yawa a ciki har a kasa ci don haka kadan zaki saka ke idan da halima ki barshi kawai indai kinsa magi shike nan.

Saiki zuba ruwan kwanan naki a cikin wannan tumatir naki daya dan suyu a kasko, kici gaba da soyawa har ya soyu, saiki saka a plate 🍽.

Sahikenan aci dadi lafiya zaki iyaci da shayi ko kuma ki hada da shayi and bred.

Kiyi share zuwa daya daga ciki social 💙 meadia dake kasa saboda yan uwa su amfana.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »