Tarihin Dakta Albdullahi Umar Ganduje Na Biyu

0 405

Idan Mai Karatu na Biye damu cikin Tarihin Dakta Abdullahi Umar Ganduje Muntsaya ne a babin Fara Aikinsa, yanzu zamu Dora daga Inda Muka Tsaya.

RAYUWAR SA A SIYASA

Dokta. Ganduje saboda son tallafawa Jama’a yasanya shi shiga siyasa, ya shiga Jam’iyar National Party Of Nigeria (NPN) lokacin Jamhuriya ta biyu kuma ya kasance Mataimakin Sakatare na Jihar Kano daga shekara ta 1979 zuwa 1980, Dokta. Ganduje kuma ya koma Jam’iyar People Democratic Party (PDP) don zama Gwamna, Amma daga baya sai yazama matemakin Gwamna ga Eng. Rabiu Musa Kwankwaso a tsakanin 1999 zuwa 2003

Baya ga Mataimakin gwamna, an kuma nada shi a matsayin Kwamishinan kannan Hokumomi Daga shekara ta 2003 zuwa 2007, sannan yazam mai bada shawara na musanman ga ministan tsaro na najeriya .

Dokta Ganduje ya kuma yi aiki a matsayin memba a Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).

An kuma nada shi a matsayin ciyaman na Federal Polytechnic, Ado Ekiti a shekara ta 2008, Bugu da kari, an nada shi a matsayin Babban Sakataren zartarwa na Lake Chad Basin Commission a Ndjamena, Chadi Republic.

An zabe shi gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC a 2015 kuma ya yi abin al’ajabi a lokacin da ya fara mulki. Tarihi bazai taba mantawa da irin salon shugabancin shi na jihar Kano ba.

Hakanan kuma, Ganduje ya kuma lashe zaben Gwamnonin shekarar 2019 a karo na biyu. Yanzu shi ne gwamnan jihar Kano na yanzu har zuwa 2023.

Dokta. Ganduje ya samu matsayin gwarzo don kare martabar Fulani, an zabe shi a matsayin Shugaban TABITAL FUAKU a Najeriya kuma shine mai kula da Gabas da Tsakiyar Afirka. Dokta. Ganduje ya kuma kasance memba, a Babban Taron Siyasa na Najeriya 2006.

TAIMAKON TALAKAWA

Dokta Ganduje ya yadda da tallafawa marasa galihu a cikin al’umma , hakan ce ta sanya shi ya kafa GANDUJE FOUNDATION.

Nan muka kawo karshe, kadda a manta idan anga wani gyara a sanar mana saimu gyara.

WhatsApp: 09012974901

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »